Uwa da 'ya'yanta guda biyu sun kashe kansu bayan 'yan uwansu sun dora musu karan tsana sakamakon mutuwar mijinta

Uwa da 'ya'yanta guda biyu sun kashe kansu bayan 'yan uwansu sun dora musu karan tsana sakamakon mutuwar mijinta

- Abubuwa na kara ta'azzara a kasar India sakamakon kashe kansu da mutane ke yi sanadiyyar cutar coronavirus

- A ranar Larabar nan da ta gabata ne, wata mata da 'ya'yanta guda biyu suka kashe kansu ta hanyar fadowa daga saman gada, sakamakon cutar coronavirus da ta kashe mijinta

- Sun kashe kansu ne sanadiyyar karan tsana da 'yan uwansu da abokanai suka dora musu

Mata da ya'yan wani mutumi da ya mutu sanadiyyar kamuwa da cutar coronavirus, suma an ruwaito cewa sun kashe kansu, bayan 'yan uwansu da abokanansu sun dauki karan tsana sun sanya musu.

Matar mai suna Parimi Snuneetha, mai shekaru 50, da ya'yanta Narasaiah Phanikumar, mai shekaru 25 da Lakshmi Aparna mai shekaru 23, sun kashe kansu ta hanyar hawa kan doguwar gada suka fado a Andhra Pradesh a ranar Laraba 19 ga watan Agusta.

Uwa da 'ya'yanta guda biyu sun kashe kansu bayan 'yan uwansu sun dora musu karan tsana sakamakon mutuwar mijinta
Uwa da 'ya'yanta guda biyu sun kashe kansu bayan 'yan uwansu sun dora musu karan tsana sakamakon mutuwar mijinta
Asali: Facebook

A cewar 'yan sanda bayan mutuwar mutumin mai shekaru 52, mai suna Narasaiah, wanda ya kamu da cutar coronavirus kwana hudu da suka wuce, danginshi sun shiga tashin hankali.

Jami'an 'yan sanda sunce iyalan mutumin sun shiga wani hali sakamakon halin ko in kula da 'yan uwansu suka nuna musu bayan mutuwar mutumin.

KU KARANTA: 'Yan sanda na neman wasu akuyoyi ruwa ajallo, bayan akuyoyin sun lalata musu motar da suke fita aiki da ita

'Yan sanda sun iske takardar da suka bari a cikin motarsu a kusa da gadar. Takardar ta ce dangin sun kashe kansu ne sakamakon halin da suka shiga sanadiyyar mutuwar mutumin.

'Yan sandan dai suna iya bakin kokarinsu wajen ganin sun ciro gawarwakin mutanen daga cikin ruwan.

Uwa da 'ya'yanta guda biyu sun kashe kansu bayan 'yan uwansu sun dora musu karan tsana sakamakon mutuwar mijinta
Uwa da 'ya'yanta guda biyu sun kashe kansu bayan 'yan uwansu sun dora musu karan tsana sakamakon mutuwar mijinta
Asali: Facebook

Uwa da 'ya'yanta guda biyu sun kashe kansu bayan 'yan uwansu sun dora musu karan tsana sakamakon mutuwar mijinta
Uwa da 'ya'yanta guda biyu sun kashe kansu bayan 'yan uwansu sun dora musu karan tsana sakamakon mutuwar mijinta
Asali: Facebook

Haka kuma an ruwaito cewa sakamakon cutar coronavirus din da ta shiga danginsu mutane sun dauki karan tsana sun sanya musu.

A rahoton da jaridar India Today ta ruwaito, wata mata da 'ya'yanta guda biyu suma sunyi kokarin kashe kansu sakamakon mijinta da ya mutu sanadiyyar kamuwa da coronavirus.

Mutanen garin ne dai suka ceto wadannan mutane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel