'Yan sanda na neman wasu akuyoyi ruwa ajallo, bayan akuyoyin sun lalata musu motar da suke fita aiki da ita

'Yan sanda na neman wasu akuyoyi ruwa ajallo, bayan akuyoyin sun lalata musu motar da suke fita aiki da ita

- Jami'an 'yan sanda a kasar Ingila na neman wasu akuyoyi ruwa ajallo

- 'Yan sandan dai na neman akuyoyin ne sakamakon lalata musu mota da suka yi da tsakar rana a lokacin da suke kan aiki

- 'Yan sandan sun bayar da sanarwar duk wanda yake da masaniya akan wadannan akuyoyi ya taimaka ya sanar da su

Jami'an 'yan sanda sun bazama neman duk wani mutumi da yake da labarin inda wasu akuyoyi suke da suka lalata musu motar da suke fita aiki da ita da tsakar rana.

A cewar wani jami'in dan sanda na kasar ta Birtaniya, 'yan sandan suna neman wadannan akuyoyi da suka bata musu mota, inda suka fita neman shaidu da suke da masaniya akan inda wadannan akuyoyi suke.

'Yan sanda na neman wasu akuyoyi ruwa ajallo, bayan akuyoyin sun lalata musu motar da suke fita aiki da ita
'Yan sanda na neman wasu akuyoyi ruwa ajallo, bayan akuyoyin sun lalata musu motar da suke fita aiki da ita
Asali: Facebook

A cewar 'yan sandan, an dauki hoton akuyoyin suna tsaye akan saman motar tasu a kusa da Newport a ranar Laraba 19 ga watan Agusta da rana, bayan an kira jami'an 'yan sandan yankin bayan an gano wani bam da aka dasa a wajen tun lokacin yakin duniya na biyu wanda bai tashi ba.

'Yan sandan sun nemi taimakon sojojin ruwa, wadanda suka taso tun daga Portsmouth domin taya su cire wannan bam.

Bayan 'yan sandan sun kammala cire bam din, sun koma motarsu suka tarar da ita akuyoyin sunyi mata kaca-kaca.

'Yan sandan yanzu suna tambayar ko akwai wanda ya san inda wadannan akuyoyi suke, wanda aka dauki hotonsu.

KU KARANTA: Rashin hankaline ace daliban da suka gama jami'a da sakamako mai kyau suna neman aiki - Muhammad Akanbi

'Yan sandan sun wallafa wannan rahoto a shafin ofishin 'yan sandan na Facebook, inda suka ce: "A wani fili dake yankin Newport an gano wani bam da aka dasa a wajen tun lokacin yakin duniya na biyu wanda bai tashi ba.

"Abokanan aikin mu sun gano wannan bam, kuma sun cire shi.

"Sai dai kuma akwai wasu akuyoyi da suka bata mana mota, idan kun gane wadannan masu laifi dake cikin hoton nan ku taimaka ku sanar damu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel