'Yan sanda sun kama 'yan kungiyar asiri 56 da kokon kawunan mutane

'Yan sanda sun kama 'yan kungiyar asiri 56 da kokon kawunan mutane

Mutum 56 da ake zargin 'yan kungiyar asiri ne sun shiga hannun jami'an tsaro a Calabar da Ogoja, jihar Cross River, sakamakon kama su da aka yi da kokon kan mutane.

An kama su ne a yankin Mile 8 a yayin da suke hanyarsu ta zuwa jihar Akwa Ibom. Sun shiga hannun jami'an tsaron a ranar Laraba.

Kamar yadda kwamishinan 'yan sandan jihar ya sanar, ya ce wadanda ake zargin sun hada da maza 46 da mata biyar.

Jimoh ya ce, "A ranar Litinin, na samu bayanin da ke nuna cewa wasu wadanda ake zargin 'yan kungiyar asiri ne suna tukin ganganci rike da tutoci bakake da jajaye.

"Suna hana zaman lafiya a titin Goodluck Jonathan kuma suna tunkarar Mile 8. An bi su da gaggawa kuma an kama su a Mile 8.

"A yayin da aka damkesu kuma aka kawo su hedkwata, sun tabbatar da cewa su 'yan kungiyar asiri ne daga karamar hukumar Akpabuyo, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa jihar Akwa Ibom.

"Bayan cajesu da aka yi, an samu kokon kan mutum sabbi har guda uku.

“An kama motocinsu biyu kirar Hiace masu lamba KAM 541 XA da XA 668 UGB, babura biyu, adduna biyar da kuma tutoci jajaye uku masu zanen kokon kan mutum a jiki.

"Duk sun amsa cewa daga kungiyar Nnabor suke, kuma sune suke da alhakin satar jama'a da duk wani tashin hankali da ke aukuwa a karamar hukumar Akpabuyo ta jihar.

“Rundunar za ta yi bincike a kan kokon kawunan mutanen don gano ko na su waye. An kammala kwashe bayanan wadanda ake zargin kuma za su fuskanci fushin hukuma."

'Yan sanda sun kama 'yan kungiyar asiri 56 da kokon kawunan mutane
'Yan sanda sun kama 'yan kungiyar asiri 56 da kokon kawunan mutane. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Boko Haram sun jigata, ba su iya yakar soji na minti 5 - Rundunar soji

Daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Mike Asuquo, ya bayyana cewa bai san komai game da kokon kan mutanen da aka kamasu da su ba.

A wani ci gaba makamancin hakan, NSCDC ta damke wasu mutum biyar da ake zargi da zama 'yan kungiyar asiri a jihar Cross River.

Kwamandan NSCDS, Danjuma Elisha, yayin damko wadanda ake zargin a ranar Laraba a garin Kalaba, ya ce an ganosu ne tun ranar Talata a karamar hukumar Ogoja ta jihar.

Kamar yadda yace, an kama wadanda ake zargin ne bayan samamen da aka kai musu yayin da suke rikici da kungiyoyin adawarsu.

Ya ce, "A ranar 18 ga watan Augustan 2020, an sanar da mu cewa wata kungiyar asiri tana taro a Igoli da ke Ogoja. Bayan isarmu, jami'anu sun gano kokon kawunan mutane da wasu kasusuwan da ake zargin na mutum ne.

"An damke mutum goma daga ciki kuma bayan tuhumarsu, an gano cewa suna surkullensu ne da wadannan abubuwan da aka samu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel