Ganduje ya gargadi Malamin Islamiyyan da ya bude makaranta ba tare da izini ba

Ganduje ya gargadi Malamin Islamiyyan da ya bude makaranta ba tare da izini ba

Gwamnatin jahar Kano ta gayyaci shugaban wata makarantar Islamiyya mai suna ‘Salman Faris islamiyya‘ da ke unguwar rijiyar zaki sakamakon bude makarantar da yayi sabanin umurnin gwamnati.

Tun lokacin da cutar Korona ta bulla a Kano, Gwamnati ta rufe makarantun Islamiyya saboda tsoron yaduwar cutar a jihar.

Har yanzu babu wanda aka baiwa izinin buɗe makarantu, boko ko Islamiyya.

Kamar yadda BBC ta ruwaito, shugaban hukumar da ke kula da makarantun tsangayyu da islamiya a Kano, Gwani Yahuza Gwani Danzarga ya ce sun gayyaci malamin ne biyo bayan wata takardar koke da suka samu daga iyayen yara da ke makarantar kan bude makarantar da yayi, tare da neman ɗaliban su biya wasu kuɗaɗe.

A cewar Gwani Yahuza Gwani Danzarga, Iyayen yaran sun yi korafin cewa Malamin ya bukaci iyayen su biya kudi N2000 na kayan kariya daga cutar Korona irinsu sunadarin tsaftace hannu dss.

A hirar da BBC tayi da shi, yace Malamin Islamiyyan ya amsa sammancinsu kuma ya bayar da hakuri bisa saba dokar da yayi.

A jawabinsa yace: “Ya zo da tsari da biyayya kuma ya bada hakuri, ya ce wannan ma tsautsayi ne yasa akayi shi, mun gargadeshi kuma mun nuna masa tsari kuma ya karba.”

” Mun umurceshi wannan takarda da ya rubutawa iyaye ya janyeshi.”

Ganduje ya gargadi Malamin Islamiyyan da ya bude makaranta ba tare izini ba
Ganduje ya gargadi Malamin Islamiyyan da ya bude makaranta ba tare izini ba
Asali: UGC

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel