Riham Yaqoob: Kyakkyawar budurwa da aka harbe a kasar Iraqi a yayin da take kokarin kare hakkin al'ummar kasar
Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun harbe wata kyakkyawar budurwa mai suna Riham Yaqoob a birnin Basra, biyo bayan zanga-zangar da take jagoranta dake kalubalantar gwamnatin kasar
Riham Yaqoob, wata kyakkyawar budurwa ce 'yar kasar Iraqi da take rajin kare hakkin dan adam, kuma likita ce da ta jagoranci zanga-zangar nuna rashin goyon baya ga gwamnatin kasar.
A ranar Laraba 19 ga watan Agustan nan ne dai aka harbe budurwar a garin Basra dake kasar ta Iraqi.

Asali: Facebook
Bayan harbe Riham, firaim ministan kasar Mustafa al-Kadhimi ya kori shugaban hukumar 'yan sandan birnin na Basra da kuma wasu daga cikin jami'an tsaro. Haka kuma yayi alkawarin yin iya bakin kokarinshi wajen tabbatar da cewa jami'an tsaro sunyi abinda ya kamata.
Firaministan ya ce:
"Abinda 'yan bindigar suka yi da kuma barazanar da suka zama baza mu yadda da ita ba, saboda haka zamu yi duk abinda ya kamata daga kan ma'aikatar cikin gida ma'aikatar tsaro waje domin ganin sun tashi tsaye wajen kare al'umma da dukiyoyinsu daga 'yan ta'addar."

Asali: Facebook
KU KARANTA: Na yiwa mijina dukan tsiya ne saboda yana raina mini wayo da yawa - Matar aure ta sanar da kotu
Wannan dai na zuwa ne watanni biyar kacal bayan Kadhimi, tsohon shugaban tsaron ya shiga ofis bayan murabus da magabacinshi yayi akan zanga-zangar da ake yi a garin Baghdad babban birnin kasar, birnin Basra da kuma wasu daga cikin biranen kudancin kasar.
Ana cigaba da zanga-zanga a Iraqi sakamakon cin hanci da yayi kaka gida a kasar, rashin aikin yi da dai sauran su.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng