Da duminsa: Buhari da shugabannin ECOWAS za su shiga ganawa ta musamman

Da duminsa: Buhari da shugabannin ECOWAS za su shiga ganawa ta musamman

Shugabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen Afrika ta kudu (ECOWAS), za su shiga ganawa ta musamman a kan halin da siyasar kasar Mali take ciki.

Daraktan fannin yada labarai na ECOWAS ne ya sanar da hakan a garin Abuja a ranar Laraba.

An kira ganawar ta gaggawa wacce za a yi ta yanar gizo, sakamakon juyin mulkin da dakarun sojin kasar Mali suka yi a ranar Talata.

Sojin hamayya sun damke shugaban kasar Mali, Boubacar Keita tare da Firayim minista Boubou Cisse a ranar Talata, inda suka tafi da su wata babbar barikin sojoji da ke wajen babban birnin jihar na Bamako.

Daga bisani, shugaban kasa Keita ya snaar da yin murabus dinsa don gujewa zubar da jini.

Da gaggawwa ECOWAS ta yi martani inda ta dauka alkawarin rufe dukkan iyakokin kasashen da ke karkashinta da kasar Mali, sannan kasar za ta fuskanci ladabtarwa bayan dakatar da ita da aka yi daga kungiyar.

Kungiyar kasashe 15, wacce ta hada da kasar Malin, ta dakatar da kasar daga shiga cikin mahukuntan kungiyar.

Da duminsa: Buhari da shugabannin ECOWAS za su shiga ganawa ta musamman
Da duminsa: Buhari da shugabannin ECOWAS za su shiga ganawa ta musamman. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Matar aure 'yar Najeriya ta sanar da yadda ubangidanta dan Faransa ya yi yunkurin lalata da ita

A watan da ya gabata, ECOWAS ta yanke hukuncin hada gwamnatin hadin guiwa yayin da take bada goyon baya ga shugaban kasa Keita, amma kuma 'yan hamayya sun soki hakan.

Gwamnatin tarayya a jiya ta kushe wannan juyin mulkin tare da kira ga ECOWAS da ta gaggauta daukar matakin da ya dace.

Ta kara da bada umarni na gaggauta mayar da shugabannin kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar.

Ministan harkokin waje na Najeriya, Geoffrey Onyeama, a wata wallafa, ya ce: "Gwamnatin Najeriya ta soki juyin mulkin da ya faru a kasar Mali a ranar Talata kuma ta bukaci gaggauta mayar da damokaradiyya.

"Muna jiran hukuncin gaggawa daga ECOWAS."

Sakataren majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres, ya bukaci gaggauta mayar da Keita da Cisse kan karagar mulkin.

Ya sanar da cewa, masana diflomasiyya na New York sun ce hukumar tsaro za su yi taron gaggawa a kan hakan a ranar Laraba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng