Bidiyo da hotunan yarinyar da fasto ya sace na tsawon shekaru 7, ta dawo gida
Sadiya Idris yarinya ce mai shekaru 19 a halin yanzu, wacce ta bace a 2013 a garin Kaduna kuma ta dawo gida a shekarar 2020. Matashiyar budurwar ta dawo gida bayan shekaru bakwai da ta kwashe bata gida.
A wata tattaunawar da ta yi da Legit TV, ta bayyana asalin abinda ya faru a yayin da ta bar gida.
Babu shakka dawowar Idris ta zo da tambayoyi masu tarin yawa saboda duk wanda ya san ta da labarin bacewarta zai so sanin abinda ya ke faruwa.

Asali: UGC
An gano cewa wani Fasto mai suna Jonah Gangas, wanda a halin yanzu yake hannun 'yan sanda ne ya saceta.
Idris ta gudu daga gida a lokacin da take da shekaru 12 kacal a duniya. Bata san dadin soyayyar mahaifiya ba, lamarin da yasa ta yanke hukuncin barin gida don rayuwa ita kadai.
A yayin da take yawo, ta fada hannun wani mutum wanda ya zo da zummar taimakonta. Mutumin ya mika ta hannun wani fasto wanda ya karbeta kuma ya mayar da ita Kirista. Ya saka ta a makaranta inda suka koma garin Jos.

Asali: UGC
Yarinyar ta ce ba za ta iya sanar da abinda yasa ta bar gida ba, kuma ba tirsasata uban rikonta yayi ba ta koma Kirista. Bayan da faston ya karbeta, bai kai wa 'yan sanda rahoto ba kuma bai mika ta ga dangiinta ba.
KU KARANTA: Yadda matashi ya saka karamar yarinya a cinyarsa, ya dinga lalata da ita
A yayin tattaunawa, Abubakar Awwal, shugaban sashen korafi ya bayyana wasu al'amura. Ya ce ba za a bar lamarin ba. Zai yuwu faston yana da niyya mai kyau na riketa, amma ba haka ya kamata ya yi komai ba. Akwai take hakki a cikin al'amarin.
A yayin da aka tambayeta ko an ci zarafinta a yayin da bata gida, ta ce a'a kuma ana matukar kula da ita. A takaice kamar diyar cikinsa ya riketa kuma yana biya mata dukkan bukatun da ta bijiro da su.

Asali: UGC
Amma kuma komawarta addinin Kirista shine babbar matsalar da ta taba addininta na farko da kuma al'adarta. A halin yanzu, ana tuhumar faston da laifin satar yarinyar a gaban kotu.
Yarinyar ta bayyana tsananin farin cikin da take ciki bayan dawowarta gida domin ta hadu da mahaifiyarta da kannanta. Dama can a hannun kakarta ta girma kuma tana samun ganin mahaifiyarta ne a yayin hutu.
Mahaifiyarta ta bayyana yadda hawan jini ya kashe mahaifin Sadiya da kakarta sakamakon batanta tare da mawuyacin halin da ta fada bayan rabuwarta da diyarta na tsawo shekaru bakwai.
Ga masu niyyar taimakonta na cigaba da karatun Boko da samun yin na addini, zaku iya tuntuban lambobin nan:
Yayanta - Aminu 0906 841 1312
Mijin Mahaifiyarta - 0806 322 4556
S
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng