Kotu ta bada umarnin kai Saratu Ya'u matar da ta kashe danta gidan mahaukata

Kotu ta bada umarnin kai Saratu Ya'u matar da ta kashe danta gidan mahaukata

- Wata babbar kotun jihar Kano ta ingiza keyar wata mata mai suna Saratu Ya'u zuwa asibitin mahaukata bayan kamata da laifin kisa

- Kotun dai ta kama Saratu da laifin kashe dan data haifa mai suna Buhari Abubakar mai shekaru biyar kacal a duniya

- Haka kuma kotun ta daga cigaba da sauraron karar matar har zuwa lokacin da sakamakon gwajin kwakwalwar da za ayi mata zai fito, wanda zai fito a watan oktoba

A ranar Laraba ne babbar kotun jihar Kano ta bayar da umarnin, a kai Saratu Ya'u, asibitin mahaukata domin ayi mata gwajin kwakwalwa, bayan an kamata da laifin kashe danta Buhari Abubakar, mai shekaru biyar kacal a duniya.

Matar mai shekaru 27 a duniya ta aikata wannan mummunan aiki a ranar 12 ga watan Yulin shekarar 2018, a kauyen Sabon Birni dake cikin karamar hukumar Gwarzo a cikin jihar Kano.

Sai dai kuma Alkalin kotun, Ibrahim Karaye, ya daga sauraron karar har zuwa ranar 8 ga watan Oktobar shekarar nan ta 2020, wato daidai lokacin da sakamakon gwajin kwakwalwar da aka yiwa matar zai fito.

Kotu ta bada umarnin kai Saratu Ya'u matar da ta kashe danta gidan mahaukata
Kotu ta bada umarnin kai Saratu Ya'u matar da ta kashe danta gidan mahaukata
Asali: Twitter

A wani labari makamancin haka kuma, Legit ta kawo muku rahoton jami'an 'yan sanda a jihar Legas sun cafke wani mutum da ke ikirarin zama basarake mai shekaru 72 mai suna Lateef Olarinde, dan shi da wasu mutum uku a kan zarginsu da ake da kashe-kashe tare da wasu ayyukan tada tarzoma a birnin Oguntedo da ke jihar.

KU KARANTA: Tserewar mai laifi: Matasa sun yi wa 'yan sanda ruwan duwatsu yayin zanga-zanga

Sauran mutum hudun sun hada da Yusuf Olarinde mai shekaru 38, Kazeem Sadiku mai shekaru 35, Sanni Olarinde mai shekaru 37, Ayomide da Babatunde Lateef.

Kamensu ya biyo bayan korafe-korafen mazauna yankin a kan miyagun ayyukan Olarinde da sauran 'yan kungiyarsa da kuma umarnin da 'yan sandan suka samu daga kwamishinan 'yan sandan jihar, Hakeem Odumosu, na su damko wadanda ake zargi.

Jami'an 'yan sandan sun ce Olarinde ya kasance cikin wadanda ake nema ido rufe a yankin, sakamakon kisan kai da tada tarzoma.

An gano cewa, daya daga cikin 'ya'yansa ya shiga hannun 'yan sanda kusan wata daya da ya gabata, kuma bayanansa ne suka sa aka kama mahaifinsa a ranar 21 ga watan Yulin 2020.

A yayin damko wadanda ake zargin a gaban manema labarai, kwamishinan 'yan sandan jihar Legas, Hakeem Odumosu, ya kwatanta Olarinde da shugaban "gagarumar kungiyar 'yan ta'addan da ta addabi yanki da kewaye."

Odumosu ya ce, an samu gawar wani mutum daya da ake zargin Olarinde da yaransa ne suka kashe kuma suka kona shi don batar da kamanninsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel