Yanzu-yanzu: Kwamishinan Kasuwanci na Bauchi, Mohammed Alhassan Sadiq ya yi murabus

Yanzu-yanzu: Kwamishinan Kasuwanci na Bauchi, Mohammed Alhassan Sadiq ya yi murabus

Kwamishinan Kasuwanci da Masana'antu na jihar Bauchi, Honarabul Mohammed Alhassan Sadiq ya yi murabus.

Hon. Sadiq ya sanar da murabus dinsa ne a daren ranar Laraba a shafinsa na dandalin sada zumunta ta Facebook.

"Duk abinda ke da farko yana da ƙarshe, a ranar 19 ga watan Agustan 2020, na ajiye aiki na a matsayin Kwamishina (Kasuwanci da Masana'antu) kuma mamba na Kwamitin Zartarwa na gwamnatin jihar Bauchi," kamar yadda Kwamishinan ya rubuta a shafinsa .

Yanzu-yanzu: Kwamishinan Kasuwanci na Bauchi ya yi murabus
Yanzu-yanzu: Kwamishinan Kasuwanci na Bauchi ya yi murabus
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kwanel Assimi Goita ya naɗa kansa shugaban ƙasa na mulkin soja a Mali

A halin yanzu dai tsohon Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayya, Hon. Yakubu Dogara ba ya shiri da gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed.

Ina mika godiya ta ga Mai Girma Gwamna Senata Bala A. Mohammed bisa damar da ya bani. "Kazalika, ina godiya ga mai gida na Rt. Hon. Yakubu Dogara saboda goyon bayansa da taimakon da ya min."

"Ina godiya ga abokan aiki na a ma'aikatar wadanda muka yi aiki tare.

"Na gode bisa karamci da aka nuna min. Ina rokon Allah ya yafe min kura-kuren da na yi kuma ina rokon gafarar al'umma. Ina rokon ku taya ni addu'a Allah ya bani sa'a. Nagode, Allah ya yi muku albarka," kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Facebook.

An dai ce Yakubu Dogara ne uban gidan siyasar Hon. Sadiq.

Idan za a iya tunawa rikicin siyasa ta kaure tsakanin Gwamna Bala Mohammed da Yakubu Dogara hakan yasa Dogara ya koma jam'iyyar sa ta APC.

Dogara ya ce ya koma APC ne saboda gwamnan Bauchi mai ci yanzu ya gaza cika wasu alƙawurra da aka yiwa al'umma bugu da kari ga rashin girmama sarakuna da rashawa da sauransu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel