Mutane 106 sun kubuta daga hannun 'yan Boko Haram

Mutane 106 sun kubuta daga hannun 'yan Boko Haram

Dakarun rundunar sojojin hadin gwuiwa (MNJTF) da ke N'Djamena, babban birnin kasar Chadi, sun karbi fararen hula 106 da suka samu kubuta daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram sannan su ka mika wuya ga rundunar soji.

Daga cikin jimillar mutanen 106 akwai 94 'yan asalin Najeriya, 11 'yan asalin kasar Kamaru, da kuma mutum guda daga kasar Chadi.

Da ya ke mika 'yan Najeriya a hannun gwamnatin jihar Borno, kwamandan MNJTF, Manjo Janar Ibrahim Yusuf, ya ce wasu daga cikin mutanen sun kai kansu zuwa hedikwatar MNJTF ta farko da ke gabashin kasar Kamaru.

Ya kara da cewa bayan wadanda suka mika wuyan, an kubutar da kananan yara da mata daga hannun mayakan.

Kwamandan ya bayyana cewa irin wannan nasara ba tana nufin cewa dakarun soji za su sassauta wajen farautar mayakan kungiyar Boko Haram ba.

Kazalika, ya bayyana cewa za su gudanar da bincike a kan mutanen da suka mika wuya ga rundunar MNJTF domin gano irin alakar da ke tsakaninsu da mayakan kungiyar Boko Haram.

Mutane 106 sun kubuta daga hannun 'yan Boko Haram
Wasu mutane da sojoji suka kubutar daga hannun 'yan Boko Haram
Asali: Depositphotos

A nasa jawabin, kwamishinan shari'a na jihar Borno, Kaka Shehu Lawan, ya ce gwamnatin jihar Borno za ta mika 'yan Najeriya hannun gwamnatin tarayya domin basu horon sauyin tunani kafin su koma cikin jama'a.

DUBA WANNAN: Buhari ya amince da kashe N3.9bn domin kammala wasu aiyuka a jihohi biyar

Ya kara da cewa, amma kafin hakan; "gwamnati za ta nemo tare da tattara dukkan bayanan da ta ke bukata a kan 'yan Najeriya da mu ka karba," a cewarsa.

Kwamishinan ya bayyana cewa damar mika wuya na daga cikin hanyoyin da gwamnati ta dauka domin kawo karshen aiyukan 'yan ta'adda.

40 daga cikin mutanen da aka kubutar kananan yara ne, 17 mata, sauran kuma maza ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng