Sabon hari: Rayuka 9 sun halaka a Niger sakamakon harin 'yan bindiga

Sabon hari: Rayuka 9 sun halaka a Niger sakamakon harin 'yan bindiga

Akalla mutum 9 da suka hada da dakarun sojin Najeriya 3 suka rasa ransu sakamakon harin 'yan bindiga a Tashan Kare da Yakila da ke karamar hukumar Rafi ta jihar Niger.

Kokarin tuntubar 'yan sandan jihar ya gagara saboda kakakin rundunar, ASP Wasiu Abiodun, baya daukar wayarsa kuma baya martani ga sakonnin da aka tura masa, Channels TV ya wallafa.

Amma kuma a wata takardar da shugaban fannin yada labarai na hedkwatar tsaro, Manjo janar John Enenche, ya fitar a shafinsu na yanar gizo, ya ce dakarun Operartion Whirl Punch sun yi musayar wuta da 'yan bindigar.

Sun kashe 'yan bindigar da ba a san adadinsu ba amma dakarun soji uku sun rasu inda wasu biyun suka samu miyagun raunika.

Kamar yadda Manjo janar Enenche ya ce, "A kokarin ci gaba da ganin bayan duk wasu 'yan ta'adda da ke yankin arewa ta tsakiya a kasar nan, dakarun rundunar Operation WHIRL PUNCH, sun samu manyan nasarori.

"Bayan bayanan sirri, sun kai wa 'yan bindigar daji hari a Tashan Kare da ke jihar Neja.

"Rundunar ta gaggauta zuwa wurin inda ta hadu da 'yan bindigar. Zakakuran sojin sun yi musayar wuta da 'yan bindigar inda suka kashe marasa adadi yayin da sauran suka tsere a gigice.

"Abun alhinin shine yadda muka rasa rayukan dakaru 3, kuma biyu suka samu miyagun raunika. Ana ci gaba da bincike kuma karin bayani zai biyo baya."

Sabon hari: Rayuka 9 sun halaka a Niger sakamakon harin 'yan bindiga
Sabon hari: Rayuka 9 sun halaka a Niger sakamakon harin 'yan bindiga. Hoto daga The Guardian
Asali: UGC

KU KARANTA: Tsohon gwamna a Najeriya ya yi kaca-kaca da karuwarsa, 'yan sanda sun damkesu

Amma kuma, rundunar 'Yan sandan jihar Niger ta tabbatar da cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun sace wani dan kasan waje da yan Najeriya a tsakanin kauyukan Yankila da Regina a karamar hukumar Rafi ta jihar.

Adamu Usman, kwamishinan yan sandan jihar ne ya tabbatar da afkuwar lamarin yayin hirar da kamfanin dillancin labarai ta Najeriya, NAN, ta yi da shi a ranar Talata a garin Minna.

Usman ya ce a ranar 17 ga watan Agusta kimanin karfe 11.05 mun samu rahoton cewa 'yan bindiga sun kai hari sun sace ma'aikatan kamfanin gine gine ta Transparent.

Ya ce wadanda ake sace din suna kula da aikin gyaran wuraren da suka lalace ne a titunan gwamnatin tarayya a jihar.

"Ba su sanar da rundunar yan sanda cewa suna aiki a jihar ba. Wannan abin da ya faru ne yasa muka san cewa suna jihar.

"Tuni mun aike da tawagar jami'an mu domin a ceto wadanda aka sace," a cewar Mr Usman.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel