Tsohon gwamna a Najeriya ya yi kaca-kaca da karuwarsa, 'yan sanda sun damkesu
Tsohon gwamnan jihar Imo, Ikedi Ohakim, ya yi kaca-kaca da wata budurwa da ake zargin karuwarsa ce amma yanzu take barazana ga rayuwarsa.
Kamar yadda rahoto daga Premium Times ya bayyana, Ohakim, wanda ya yi shugabancin jihar Imo daga 2007 zuwa 2011, yana soyayya da Chinyere Amuchienwa.
Budurwar na zama a jihar Legas inda take kasuwancin kayan sawa. Ana zargin cewa alakarsu ta baci ne bayan da Amuchienwa ta yi kokarin bata masa suna, lamarin da yasa ya kira mata 'yan sanda.
Budurwar ta zargi tsohon gwamnan da bata zoben lu'u-lu'u amma na bogi don saka ranar bikinsu.
Ohakim yana da shekaru 63 a duniya kuma yana da mata mai suna Chioma wacce suka kwashe shekaru 39 da yin aure. Suna da 'ya'ya biyar da jikoki.
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan sanda sun garkame wani fitaccen otal a Abuja (Bidiyo)
A wata takardar korafi da tsohon gwamnan ya mika ga sifeta janar na 'yan sandan Najerya, Mohammed Adamu, Ohakim ya ce, "A ranar Asabar, 18 ga watan Janairun 2020, Chinyere ta ci zarafina.
"Ta yaudareni inda ta bukaci ganina. Daga bisani na gayyaceta dakin otal dina da Asokoro a Abuja inda ta iso wurin karfe 8:15 na yamma.
"Ina bude kofa ta hau ni da duka har da shako wuyan rigata da dukkan karfinta. Ban yi sanya ba na tureta."
Ohakim ya ci gaba da cewa, "A yayin da nake kokarin tashi, ta yi kokarin kwace wayata amma na karba da karfi. Ta gaggauta daukar jakarta inda na yi zaton bindiga za ta fito da ita."
Ohakim ya ce da gaggawa ya fita yana ihun neman taimako. A cewarsa, za a iya amfani da CCTV ta otal din wurin tabbatar da ikirarinsa.
Daga nan ne ya kira jami'an 'yan sanda da ke ofishinsu na Asokoro don kama karuwar ta shi.
Tsohon gwamnan ya tabbatar wa da 'yan sanda cewa Amuchienwa na da shekaru 56 a duniya kuma bazawara ce.
Ya ce Amuchienwa ta kasance kawarsa wacce ya ke yi wa alfarmma daban-daban, kuma ta kasance daya daga cikin wadanda suka yi ruwa da tsaki wurin yakin neman zabensa.
Amma ya ce, wannan alakar ta lalace kuma tuni take yunkurin bata masa suna tare da ganin bayansa.
Ya ce ya matukar razana kuma yana son shugaban 'yan sandan Najeriya ya shiga lamarin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng