Da duminsa: 'Yan sanda sun garkame wani fitaccen otal a Abuja (Bidiyo)

Da duminsa: 'Yan sanda sun garkame wani fitaccen otal a Abuja (Bidiyo)

- Jami'an runduna ta musamman ta sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, sun garkame otal na Stonehedge da ke Abuja

- Duk da basu bayyana dalilinsu na yin hakan ba, an gano cewa baraka ce aka samu tsakanin Magajin Garin Sokoto da gwamnatin jihar Zamfara

- Daga isarsu, sun fatattaki matukan jiragen sama 12, wasu mutum 26 da suka samu tare da ma'aikata kusan 100 na otal

Jami'an 'yan sanda daga hedkwatarsu da ke Abuja sun garkame otal na Stonehedge da ke babban birnin tarayyar, jaridar The Nation ta wallafa.

Wani kamfani mallakin Magajin Garin Sokoto, Alhaji Hassan Danbaba ke kula da shi a madadin gwamnatin jihar Zamfara.

Jami'an 'yan sandan dauke da bindigogi sun tsinkayi otal din wurin karfe 10:12 na safiyar Talata, inda suka fatattaki matuka jirgin sama 12 tare da wasu baki 26.

Matuka jiragen saman ma'aikata ne a kamfanonin MaxAir da Azman Air.

Kusan ma'aikata 10 da ke aiki 'yan sandan suka fatattaka, umarni daga rundunar sifeta janar na 'yan sandan Najeriya.

Da duminsa: 'Yan sanda sun garkame wani fitaccen otal a Abuja (Bidiyo)
Da duminsa: 'Yan sanda sun garkame wani fitaccen otal a Abuja (Bidiyo). Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ka fada wa jama'a malaman da ke son kudi ko ka rufe mana baki - Fasto ya caccaki El-Rufai

Duk da 'yan sandan basu bayar da dalilin garkame otal din ba, kuma basu bada wata takardar shaida daga kotu ba, an gano cewa akwai wani rikici tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da kamfanin Magajin Garin.

An gano cewa tsohon ofishin gwamnatin jihar Zamfaran na kamfanin Magajin Garin ne kuma sun karba hayarsa tun a 2009.

Amma kuma rikicin da aka samu a kan hayar yana gaban wata babbar kotun tarayya.

A ranar 31 ga watan Oktoban 2019, Mai shari'a Yusuf Halilu, ya bada umarnin da ya haramtawa gwamnatin jihar Zamfara daukar wani mataki na kwacewa ko take yarjejeniyar da ke tsakaninsu har sai an kammala shari'ar.

Alkalin ya bada umarnin wucin gadi da ke haramta wa gwamnatin jihar Zamfara shiga sabgar Magajin Garin a harkar mallaka ta kadarar.

Daya daga cikin matukan jirgin ya ce: "An bukace mu da mu gaggauta barin otal din kuma bamu da wani zabi da ya wuce yin hakan.

"Abin takaici ne da kunya. Muna zaton karantsaye ne aka samu a kan tsaro amma daga baya sai muka gane cewa rikici ne."

Ga bidiyon yadda lamarin ya kasance:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel