Soji sun kashe 'yan bindiga 3, sun ragargaza sansaninsu 12 a Katsina

Soji sun kashe 'yan bindiga 3, sun ragargaza sansaninsu 12 a Katsina

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta halaka wasu mutum uku da take zargin 'yan bindiga ne kuma ta ragargaza sansaninsu 12 da ke kauyen Yobe Baranda da ke karamar hukumar Batsari ta jihar.

Mukaddashin daraktan yada labarai na ma'aikatan tsaro, Birgediya janar Bernard Onyeuko ne ya sanar da hakan a yayin da ya yi magana a kan ayyukan rundunar Operation Sahel Sanity.

Onyeuko ya sanar da hakan a ranar Litinin yayin jawabi ga manema labarai a kan ayyukan rundunar da ke karamar hukumar Faskari.

Ya kara da cewa rundunar sun damke wani mai kawo wa 'yan bindigar makamai wadan daga baya ya rasu sakamakon ciwon sukari.

Ya ce: "A ranar 12 ga watan Augustan 2020, a wani samame na hadin guiwa, rundunar ta ragargaza sansani 12 na 'yan bindiga da ke kauyen Yobe Baranda a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

''Yan bindiga uku sun rasa rayukan su a wannan harin inda wasu suka tsere da miyagun raunika."

Soji sun kashe 'yan bindiga 3, sun ragargaza sansaninsu 12 a Katsina
Soji sun kashe 'yan bindiga 3, sun ragargaza sansaninsu 12 a Katsina. Hoto daga The Guardian
Asali: UGC

KU KARANTA: Boko Haram: Sojoji sun ragargaza maboya da kayan aikin 'yan ta'adda a Borno

Ya ce dakarun rundunarta da ke karamar hukumar Sabon Birni na jihar Sokoto a ranar 15 ga watan Augusta, sun yi nasarar kama masu kai wa 'yan bindigar makamai. Suna shigowa yankin arewa maso yamma daga kasashe masu makwabtaka.

"An kama Alhaji Adamu Alhassan, Salisu Adamu da Abdullahi Sani duk 'yan kasar Nijar, da miyagun makamai a Dantudu da ke yankin Mailailai a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

"An samesu da AK 47 shida, harsasanta zagaye 3 da kuma harsasai na musamman 2,415 wadanda suka hoye a ababen hawansu.

"Binciken farko ya bayyana cewa suna kan hanyarsa ta kai wa 'yan bindiga ne da ke karamar hukumar Isah ta jihar Sokoto.

"Alhaji Adamu Alhassan na fama da ciwon sukari da hawan jini. Hakan yasa ya rasu a yayin da da yake hannun zakakuran dakarun."

Har ila yau, bincike ya nuna cewa ana amfani da sauran mutum biyun wurin kamo sauran 'yan ta'addan.

Onyeuko ya ce tarin nasarorin da dakarun suka samu a cikin kwanakin na ba zai yuwu ba, ba tare da hadin kan mazauna yankin ba wadanda ke bai wa jami'an tsaron bayanai.

Ya jinjinawa dukkan mazauna yankin arewa maso yamma a kan hadin kan da suke bai wa jami'an tsaron.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel