Dalibai 24,000 suka zauna zana jarabawar WAEC a Kano

Dalibai 24,000 suka zauna zana jarabawar WAEC a Kano

Akalla dalibai 24,545 ne suka fara rubuta jarabawar fita daga sakandare (WAEC) a jihar Kano, ranar Litinin 17 ga watan Agusta, tare da bin ka'idojin takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Kamfanin dillancin labaran Nigeria (NAN) ta ruwaito cewa daga cikin 11,400 na dalibai 27,454 da suka fara rubuta jarabawar sunyi rajista a makarantun gwamnati sannan sauran 16,460 kuma sunyi rajista a makarantun kudi dake jihar.

An fara gudanar da jarabawar a cibiyoyi 538 da aka kayyade domin gudanar da jarabawar a fadin jihar.

Wani wakilin NAN wanda ya ziyarci inda ake gudanar da jarabawar a wasu daga cikin cibiyoyin, ya rahoto cewa makarantun sun samar da hanyoyin da za'a bi domin takaita yaduwar cutar COVID-19.

Wasu daga cikin makarantun da aka ziyarta sun hada da kwalejin Rumfa, GSS, Sabuwar Kofa, Makarantar Kano Capital da kwalejin Gwamnati na kano.

A mashigar makarantun an hangi abubuwan tsaftace hannu kamar su sabulu, sinadarin tsaftace hannu, ruwa da kuma na'urar gwada yanayin jiki, ana gwada dalibai da maziyarta.

NAN ta ruwaito cewa dalibai da malamai duk sun sanya takunkumin rufe fuska sannan an bada tazara a ajijuwan jarabawar.

Dalibai 24000 suka zauna rubuta jarabawar WAEC a Kano
Dalibai 24000 suka zauna rubuta jarabawar WAEC a Kano
Source: UGC

Wani ma'aikacin a kwalejin Rumfa yace anyi shirye-shirye matuka a makarantar domin tabbatar da an bi dokokin takaita yaduwar COVID-19.

"Muna da akalla dalibai 214 da zasu zauna zaman rubuta jarabawar WAEC. Babban ajin zana jarabawar yana daukar kimanin dalibai 600 a lokacin jarabawar makaranta.

"Amma saboda bada tazarar da annobar coronavirus ta haifar, musa dalibai 186 a ajin. Sai muka raba sauran dalibai 28 a ajijuwa biyu," a cewarshi.

A GGSS, Sabuwar Kofa, wani ma'aikacin makarantar yace kusan dalibai 30 ne zasu rubuta jarabawar a cibiyar.

Har ila yau, Shugaban Makarantar First Grade Comprehensive School, Jerry Adaji ya kara da cewa dalibai 30 ne zasu zauna zana jarabawar a makarantar.

Adaji yace, "A da ajin yana daukar dalibai 55 amma saboda annobar coronavirus, an rarraba daliban sha hudu hudu a kowanni aji.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel