Ka fada wa jama'a malaman da ke son kudi ko ka rufe mana baki - Fasto ya caccaki El-Rufai

Ka fada wa jama'a malaman da ke son kudi ko ka rufe mana baki - Fasto ya caccaki El-Rufai

Fasto Johnson Suleman, babban Faston cocin Omega Fire Ministries, ya yi martani ga ikirarin gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, na cewa wasu shugabannin kudancin Kaduna na bukatar "ambulan" daga gwamnatinsa kafin zaman lafiya ya wanzu.

A cikin kwanakin karshen mako, Gwamna El-Rufai ya bayyana a gidan talabijin na Channels, inda ya zargi shugabannin kudancin Kaduna da bukatar kudi don hana kashe-kashen yankin.

A yayin martani ga wannan tsokacin, Fasto Suleman ya kalubalanci gwamnan da ya bayyana sunayen shugabannin ko kuma ya rufe wa jama'a baki kuma ya gyara matsalar da ke jihar.

A martanin da ya yi ta shafinsa na Twitter, Suleman ya ce, "Na ji cewa wasu masu ruwa da tsaki a Kaduna na bukatar 'ambulan', shiyasa suke ruruta wutar rikici.

"Idan ka tabbatar da ikirarinka, bayyana sunayensu ta yadda za mu fito da su kan titin. Idan ba haka ba, ka rufe bakinka kuma ka gyara matsalar. Zubar da jinin ya isa haka."

Ka fada wa jama'a malaman da ke son kudi ko ka rufe mana baki - Fasto ya caccaki El-Rufai
Ka fada wa jama'a malaman da ke son kudi ko ka rufe mana baki - Fasto ya caccaki El-Rufai. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Batanci ga Allah: Kotu ta yanke wa yaro mai shekaru 13 hukunci mai tsanani

Nasir El-Rufa'i, gwamnan jihar Kaduna, ya ce gwamnotocin jihar na baya su kan biya wasu shugabanni a kudancin jihar Kaduna da ake zargin suna rura wutar kashe-kashe a yankin.

El-Rufa'i ya bayyana cewa ba zai biya bukatar 'yan ta'adda ta hanyar basu kudi ba, sai dai ya tabbatar da cewa an gurfanar da duk wanda aka samu hannunsa a cikin kashe-kashen jama'a a kudancin Kaduna.

Da ya ke magana a wani shirin gidan talabijin na 'Channels', gwamnan ya bayyana cewa gwamnatocin baya na bawa shugabannin yankin kunshin kudi domin kar a samu barkewar rikici.

Duk da yawan jami'an tsaro da gwamnati ta tura zuwa kudancin jihar Kaduna, har yanzu ana cigaba da samun rahoton kai hare-hare masu nasaba da kabilancin a yankin.

Wasu sun zargi gwamna El-Rufa'i da nuna bangaranci da halin 'ko in kula' a kan halin rashin tsaro da kudancin Kaduna ke ciki.

Amma yayin da ya ke magana a shirin gidan talabijin din Channels, El-Rufa'i ya ce wasu daga cikin shugabannin yankin su na jin haushinsa saboda ya dakatar da biyansu wadancan kudade da su ka saba karba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel