Hukuncin kashe matashi saboda batanci: Kungiya ta rubuta wasika zuwa Ganduje, Buhari, da Amurka

Hukuncin kashe matashi saboda batanci: Kungiya ta rubuta wasika zuwa Ganduje, Buhari, da Amurka

Wata kungiya mai rajin kare dimokradiyya, 'Concerned Nigerians', ta rubuta wata wasika zuwa ga gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ofishin jakadancin kasar Amurka.

Kungiyar ta rubuta wasikar ne domin nuna rashin amincewa da hukuncin kisa da wata kotun Shari'ar Musulunci a jihar Kano ta yankewa Yahaya Sharif Aminu,wani matashi da ke wakokin yabon Inyass.

A cikin wasikar da suka aika zuwa ofishin gwamnan jihar Kano, shugaban kasa, da ofishin jakadancin Amurka, kungiyar ta bayyana cewa hukuncin kotun ya sabawa adalci da aiki da hankali da tunani.

A cikin wani jawabi da shugabanta na kasa, Deji Adeyanju, ya fitar, kungiyar ta yi alla-wadai da kokarin yin amfani da jami'an tsaron kasa domin yin aikin addinan da basu da matsunguni a kundin tsarin mulkin kasa.

"Kundin tsarin mulkin kasa ya haramta 'yan sandan addini a karkashin sashe na 10, sannan bai rungumi wani addini a matsayin na kasa ba.

"Sashe na 38 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tabbatarwa da duk 'yan kasa 'yancin tunani, addini da kuma 'yancin sauya addini ko abin bautar da mutum ya yarda da shi."

Hukuncin kashe matashi saboda batanci: Kungiya ta rubuta wasika zuwa Ganduje, Buhari, da Amurka
Hukuncin kashe matashi saboda batanci: Kungiya ta rubuta wasika zuwa Ganduje, Buhari, da Amurka
Asali: Twitter

"Mu na kira ga shugaban kasa da ofishin jakadancin kasar Amurka a kan su roki gwamnan jihar Kano don ya ceci wannan matashi daga rashin adalcin da aka yi masa da kuma tserar da rayuwarsa wacce yanzu haka ke cikin hatsari a gidan yari na Kano inda ake tsare da shi," a cewar kungiyar.

A ranar Litinin, 10 ga watan Agusta, wata babbar kotun Shari'a da ke zamanta a Hausawa Filin Hockey da ke cikin birnin Kano ta zartar da hukuncin kisa ga matashin mai shekaru 22 saboda wallafa wata waka mai dauke da kalaman batanci ga Annabi Muhammad.

DUBA WANNAN: Bidiyo: Budurwa ta ki karbar kyautar motar N66.6m saboda bata son kalar fentinta

Daily Ngerian ta wallafa cewar wata jaridar yanar gizo mai suna 'Focus' da ke Kano ta bayyana cewa alkalin kotun, Khadi Aliyu Muhammad, ya zartar da hukunci a kan matashin, Yahaya Aminu Sharif, a yau, Litinin.

Jaridar ta bayyana cewa Khadi Muhammad ya zartar da wannan hukunci ne bayan ya gamsu da hujjojin cewa matashin ya aikata laifin da ya jawo aka gurfanar da shi a gaban kotun.

An gurfanar da matashin mawaki Yahaya a gaban kotu bayan an zargeshi da wallafa wata waka mai dauke da kalaman batanci ga annabi Muhammad a cikin watan Maris na shekarar 2020.

Bayan wallafa wakar da kuma yaduwarta a dandalin sada zumunta, musamman Whatsapp, wasu fusatattun matasa sun kone gidan su matashin tare da jagorantar zanga-zanga zuwa hedikwatar hukumar Hisbah.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel