Boko Haram: Sojoji sun ragargaza maboya da kayan aikin 'yan ta'adda a Borno

Boko Haram: Sojoji sun ragargaza maboya da kayan aikin 'yan ta'adda a Borno

Rundunar sojin Najeriya a ranar Litinin, ta ce dakarun sojin sama karkashin rundunar Operation Lafiya Dole, ta halaka wasu 'yan ta'adda tare da ragargaza maboyarsu da kayan aikinsu a Tumbuma Baba da kuma Boboshe a jihar Borno.

Shugaban fannin yada labarai na rundunar, Manjo janar John Enenche a wata takarda, ya ce wannan nasarar ta samu ne sakamakon hari ta jiragen yaki da suka kai a ranar 16 ga watan Augustan 2020 a sabon atisaye mai suna "HAIL STORM".

Ya ce Hail Storm atisaye ne ta sojin sama wanda aka samar da shi don gano maboyar mayakan ta'addanci na ISWAP da Boko Haram a yankin tafkin Chadi da dajin sambisa da ke jihar Borno.

Ya yi bayanin cewa, harin da aka kai Tumbuma Baba, daya daga cikin tsibirin tafkin Chadi, an yi shi ne bayan bayanan sirri da aka samu wanda ke nuna cewa mayakan ISWAP da wasu shugabanninsu suna boyewa a cikin dajin.

Ya ce jiragen yakin dakarun sojin saman sun bazu ne da taimakon ATF inda suka yi nasarar samun maboyar. Hakan ne yasa suka halaka wasu 'yan ta'addan tare da rugurguza gine-ginensu.

Boko Haram: Sojoji sun ragargaza maboya da kayan aikin 'yan ta'adda a Borno
Boko Haram: Sojoji sun ragargaza maboya da kayan aikin 'yan ta'adda a Borno. Hoto daga Channels TV
Asali: UGC

KU KARANTA: Ruwa ya halaka wani mutum a otal bayan da ya je shakatawa da budurwarsa

Ya kara da cewa, da yawa daga cikin 'yan ta'addan sun rasa rayukansu kuma wurin zamansu ya rushe a Boboshe, wani kauye da ke gabas da dajin Sambisa wanda sojin saman suka ragargaza.

Enenche ya ce, dakarun sojin Najeriya tare da hadin guiwar sauran jami'an tsaron kasar na da masu ruwa da tsaki za su ci gaba da tsananta kokarinsu wurin ganin bayan ta'addanci a yankin arewa maso gabas na kasar nan.

A wani ci gaban makamancin hakan, daakarun sojin saman Najeriya sun ragargaza wani sansanin mayakan ta'addanci na ISWAP da ke jihar Borno, majiya daga rundunar sojin ta tabbatar.

Kamar yadda shugaban fannin yada labarai na rundunar, Manjo Janar John Enenche, ya tabbatar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Juma'a.

Ya ce sansanin 'yan ta'addan da ke Tongule a yankin tafkin Chadi da ke arewacin jihar Borno ya sha wuta daga dakarun Operation Lafiya Dole.

Enenche ya kara da cewa, sun kai samamen ne ta jiragen yaki a ranar Laraba bayan rahotonnin da suka samu daga jama'a, wanda ke nuna cewa akwai al'amuran 'yan ta'addan a kauyen.

Ya bayyana cewa, samamen na daga cikin kokarin kawo karshen ta'addanci a yankin arewa maso gabas. Hakan ya kawo karshen rayukan mayakan ISWAP a sansanin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel