Bayelsa: Diri ya yi martani a kan soke zabensa, ya sanar da matakin dauka

Bayelsa: Diri ya yi martani a kan soke zabensa, ya sanar da matakin dauka

Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya ce zai daukaka kara a kan hukuncin kotu na ranar Litinin a kan soke zaben jihar da ta yi a Abuja. Ya ce ya bai wa lauyoyinsa umarnin daukaka kara.

Diri, wanda ya yi jawabi jim kadan bayan yanke hukunci, wanda kotun ta ce hukumar zabe mai zaman kanta ta cire jam'iyyar ANDP da dan takararta a zaben 16 ga watan Nuwamban 2019.

Ya ce yana da tabbacin cewa shari'a za ta yi masa adalci inda za ta tabbatar da nasararsa daga karshe.

Diri ya ce: "Dole ne mu saka yardarmu a shari'a kuma za mu daukaka kara. Muna da tabbacin Ubangiji zai ba mu nasara.

"Wannan kotu ce ta farko kuma na bai wa lauyoyina umarnin daukaka kara. Muna da damar daukaka kara har zuwa kotun koli."

Gwamnan ya yi kira ga mambobin jam'iyyar PDP da kuma magoya bayansa da kada su tsorata kuma su ci gaba da kwantar da hankalinsu tare da kiyaye dokoki.

A wani ci gaba makamancin hakan, tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson, ya yi kira ga jama'ar jihar Bayelsa da kada su tada hankalinsu a kan hukuncin da kotun zaben ta yanke na soke zaben gwamnonin jihar da ta yi.

Bayelsa: Diri ya yi martani a kan soke zabensa, ya sanar da matakin dauka
Bayelsa: Diri ya yi martani a kan soke zabensa, ya sanar da matakin dauka. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

KU KARANTA: Ruwa ya halaka wani mutum a otal bayan da ya je shakatawa da budurwarsa

Ya kwatanta hukuncin da koma baya amma na wucin-gadi wanda ba zai shafi komai ba har sai an kai koluluwar shari'ar.

Tsohon gwamnan a takardar da ya fitar ta hannun mai basi shawara ta fannin yada labarai, Fideli Soriwei, ya ce PDP da gwamnatin jihar za ta daukaka kara.

Ya jaddada cewa babu wurin zaman wani a gidan gwamnatin jihar Bayelsa baya ga Diri, har sai shari'ar ta kai kotun koli.

Dickson ya yi kira ga jama'ar jihar Bayelsa da su ci gaba da al'amuransu ba tare da tashin hankali ba saboda hukuncin.

Ya ce: "Ina kira ga 'yan jihar Bayelsa da su kwantar da hankalinsu. Kada su fassara abinda ya faru a kotun sauraron kararrakin zaben a yau da wani abu daban.

"Wannan hukunci koma baya ne amma na wucin-gadi. Bashi da wata illa a kan halin da muke ciki tunda ana kan daukaka kara."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel