Yanzu-yanzu: Kotu ta soke zaben gwamnoni na jihar Bayelsa
Wata kotun sauraron kararrakin zabe da ke zama a Abuja, ta soke zaben jihar Bayelsa wanda Gwamna Duoye Diri na jihar Bayelsa da mataimakinsa, Lawrence Ewhrudjakpo suka yi nasara a jihar.
Alkalai uku na kotun wadanda suka samu shugabancin Mai shari'a Ibrahim Sirajo. a ranar Litinin sun sanar da wannan hukuncin bayan jam'iyyar ANDP ta zarga rashin saka ta a jerin jam'iyyu a zaben da aka yi a ranar 16 ga watan Nuwamban 2019.
Alkalan sun bayar da umarnin sake wani zaben gwamnonin a jihar a cikin kwanaki 90.
Karin bayani na nan tafe...
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng