Coronavirus: Abubuwa 3 da suka hana cutar yin tasiri a Afrika

Coronavirus: Abubuwa 3 da suka hana cutar yin tasiri a Afrika

Har yanzu ana ci gaba da samun sabbin mutane da suka haarbu da cutar korona a kasashen duniya, yayinda masu cutar da dama ke samun waraka.

Kawo yanzu dai, fiye da mutum miliyan daya ne suka kamu da cutar a nahiyar Afrika, kuma har yanzu ana samun karuwar masu kamuwa da cutar a kasashen nahiyar.

Sai dai duk da haka, Hukumar Lafiya Ta Duniya ta ce ba a kai ga gano dalilan da suka sa nahiyar take da karancin masu kamuwa da cutar ba idan aka hada su da sauran nahiyoyi na duniya.

Kasashe biyar da suka hada da Afrika Ta Kudu, Masar, Najeriya, Ghana da Aljeriya ne ke da kashi 74 cikin 100 na masu dauke da cutar ta korona a Afrika.

Coronavirus: Abubuwa 3 suka hana cutar yin tasiri a Afrika
Coronavirus: Abubuwa 3 suka hana cutar yin tasiri a Afrika Hoto: Lowell Sun
Source: UGC

Sai dai wasu masana na ganin akwai wasu dalilai na musamman da ya sa cutar ba ta yi tasiri a Afrika ba kamar yadda ta yi a sauran nahiyoyi.

KU KARANTA KUMA: Dakatar da sarakuna a kan ziyartar Buhari: Basarake ya yi martani ga gwamnan PDP

A wata hira da sashin BBC, Dakta Nasir Sani Gwarzo, wani kwararren likita ne kuma masani kan cutuka masu yaduwa, ya bayyana wasu dalilai a ya ke ganin suka sa cutar ba ta yi kamari a kasashen Afirka ba duk da a cewarsa ba a tabbatar da dalilan ba kimiyyance:

1. Yanayin zafi a nahiyar Afrika

Tun bayan bayyanar cutar korona a duniya, an ta rade-radi kan cewa rayuwa a wuri mai dumi ka iya kare mutane daga kamuwa da cutar korona, amma Hukumar Lafiya Ta Duniya ta fito fili ta ce hakan ba gaskiya bane.

Akasarin kasashen Afrika suna cikin yanayi na zafi, kuma a cewar Dakta Sani Gwarzo, "kasashe masu dumi sun dan fi samun sassauci".

Dakta Gwarzo ya dogara ne da cewa gashi an yi wata shida da bullar cutar a nahiyar ta Afrika, amma adadin wadanda suka mutu sakamakon cutar a nahiyar bai kai rabin na kasa daya da ke a sauran nahiyoyi ba.

2. Yawan matasa a Afrika

Bincike da Hukumar Lafiya Ta Duniya ta gudana, ta ce matasa ba su tsira daga kamuwa da cutar korona ba.

A cewar Dakta Gwarzo, "idan aka yi la'akari za a ga cewa matasa sun fi yawa a nahiyar Afrika, su kuma can za a ga akwai tsofaffi dayawa, wanda da cutar ta shiga, nan da nan za ta yi musu mummunar illa".

3. Yawan tafiye-tafiye na mutanen Turai

Dakta Gwarzo, ya ce akwai yiwuwar cewa yawan tafiye-tafiye da sauran mutanen nahiyoyi ke yi ya sa cutar ta fi tsanani fiye da Afrika.

"Yadda 'yan Afrika suke tafiye-tafiye, bai kai yawan yadda 'yan Turai suke tafiye-tafiye ba, yawan kasar da ta fi kowace yawan matafiya, na ƙasa da ƙasa sun fi samun wannan matsala".

Dakta Gwarzo ya ce duk da cewa wadannan dalilian da ya bayyana ba a tabbatar da su a kimiyance ba, amma ana nan ana tantance su, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel