Jigo a jami'yyar APC ta Legas, Lanre Razak ya riga mu gidan gaskiya

Jigo a jami'yyar APC ta Legas, Lanre Razak ya riga mu gidan gaskiya

Wani rahoto da Legit.ng ta yi karo da shi na nuna cewa Allah ya yi wa jigo a jami'yyar APC a jihar Legas, Lanre Razak rasuwa.

Marigayin ya rasu ne a safiyar ranar Asabar bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Ya rasu yana da shekaru 74 da haihuwa.

Rahoton ta kafar watsa labarai ta TVC ta wallafa ya kuma ce Lanre Razak na daya daga cikin mambobin kwamitin mashawartan gwamnan jihar Legas.

Majiyar ta Legit.ng ta sanar da rahoton rasuwar ne a sahihiyar shafinta na Twitter a ranar Asabar 15 ga watan Agusta.

Jigo a jami'yyar APC ta Legas, Lanre Razak ya rasu
Lanre Razak. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Alkalin da ya yi shari'ar zaben Atiku da Buhari ya samu karin girma

Sai dai kawo yanzu gwamnatin jihar ko iyalansa ba su riga sun fitar da rahoto game da rasuwarsa ba ko sanadin rasuwarsa.

Ku saurari karin bayani ..

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel