Hotunan karbar karamcin da 'yan Najerya suka yi wa Jonathan a Bamako, Mali

Hotunan karbar karamcin da 'yan Najerya suka yi wa Jonathan a Bamako, Mali

- Tsohon shugaban kasar Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan, ya ziyarci 'yan Najeriya da ke Bamako, babban birnin kasar Mali

- A halin yanzu, tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya je kwantar da tarzoma a kasar Mali

- Tsohon shugaban kasar Najeriyan ya ce ya matukar jin dadin kara da kishin kasa da 'yan Najeriya na Bamako suka gwada masa

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan, ya ziyarci 'yan Najeriya da ke Bamako, kasar Mali.

Jonathan a halin yanzu ya je kwantar da tarzoma ne kasar Afrika ta yamman. A ranar Juma'a, 14 ga watan Augusta, ya ce ya je domin kai ziyara ga 'yan kasarsa.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa ya yi matukar farincikin kara da kishin kasa da 'yan Najeriya suka nuna masa.

Goodluck Jonathan ya ziyarci 'yaan Najeriya da ke Bamako, kasar Mali
Goodluck Jonathan ya ziyarci 'yaan Najeriya da ke Bamako, kasar Mali. Hoto daga Goodluck Jonathan
Asali: UGC

KU KARANTA: Zargin gwamnan arewa da Boko Haram: Wurin 'yan kasuwar kauye na samu labari - Mailafiya

Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su kassance masu dabi'u nagari don kare sunan kasarsu ta gado a duk inda suke.

"Na samu lokaci a ziyarar da nayi kasar Mali inda na ziyarci 'yan Najeriya da ke Bamako. Na yi matukar farin ciki da kara da kishin kasa da suka nuna min.

"Ina kira garesu da su kasance masu halayya ta gari domin kare mutuncin kasarsu," yace.

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya mika sako ga matasan Najeriya a yayin da yake jinjina musu kokarin da suka yi wurin shawo kan kalubalen da ke addabarsu ballantana a yayin annobar korona.

Sannanen abu ne idan aka ce annobar korona ta zo da manyan kalubale a fadin duniya.

Tsohon shugaban kasar ya bada wannan sako ne a yayin shagalin bikina ranar matasa ta duniya wacce majalisar dinkin duniya ta fitar don matasan fadin duniya.

Jonathan ya kara da yin kira ga dukkan shugabannin nahiyar Afrika da su yi kokarin ganin sun kafa zaman lafiya tare da saka matasa a cikin tsarika ta yadda za su bada gudumaawarsu ga ci gaban nahiyar.

Wannan na kunshe ne a takardar da ya fitar ta hannun Wealth Dickson Ominabo, mai magana da yawun gidauniyar Goodluck Jonathan, don shagalin ranar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel