Rudani: Bazawara ta haifarwa mijinta tagwaye bayan mutuwarsa da shekaru uku

Rudani: Bazawara ta haifarwa mijinta tagwaye bayan mutuwarsa da shekaru uku

Wata mata mai suna Lucy Kelsall, wacce mijinta ya mutu sakamakon kamuwa da ciwon kansar makogoro, ta haifi tagwaye bayan mutuwarsa da shekaru uku.

An adana maniyyin mijin Lucy mai suna David tun kafin a yi masa aikin da ya mayar da shi 'juya'. Daga baya likitoci sun dasawa Lucy maniyyin mijinta ta hanyar IVF.

Lucy, bazawara mai shekaru 37, ta ce ta na matukar mamaki da farin cikin cewa za ta cigaba da kasancewa da wani bangare na mijinta; tunda ta haifar ma sa tagwaye, bayan mutuwarsa a shekarar 2017.

Ta haifi 'ya'yanta guda biyu cikin koshin lafiya, kuma an saka mu su suna David da Samuel.

Da ta ke magana da manema labarai a kan tsohon mijinta, Lucy ta bayyana cewa; "ya yi farin ciki da mamaki bayan na sanar da shi cewa zan haifa ma sa yaro a lokacin ya na jinyar ajali.

"Har yanzu ina tuna yadda fuskarsa ta cika da annuri bayan na sanar da shi, na san zai kasance mai matukar alfahari duk inda ya ke.

"Dukkan yaran sun debo wasu halittu irin na mahaifansu; kafafun David irin na mahaifinsa ne ma su girma, shi kuma Samuel ya gado korayen idanu irin nata," a cewar Lucy.

Rudani: Bazawara ta haifarwa mijinta tagwaye bayan mutuwarsa da shekaru uku
Rudani: Bazawara ta haifarwa mijinta tagwaye bayan mutuwarsa da shekaru uku
Asali: Twitter

A wani labari mai yanayin daure kai da ban mamaki da Legit.ng ta wallafa, wata mata mai amfani da dandalin sada zumunta ta wallafa hotunanta tare da maza biyu da yara da ta ce mazanta ne kuma suna zaune lafiya.

DUBA WANNAN: An bayyana dalilin da ya sa kasashen duniya su ka daina sayarwa da Najeriya makamai

Kenya Stevens, mace mai auren maza biyu, ta ce har yanzu tana iya tsunduma wa cikin kogin soyayya da wani namijin idan tasu ta zo ɗaya.

Ta wallafa hotunan mazanta biyu; Rakhem Seku, mai bawa mutane shawarwari kan zamantakewar soyayya kuma marubucin littafai.

Tana kiran su da sunayen 'Hubby 1' da 'Hubby 2' wato miji na farko da miji na biyu, kuma har a wasu lokutanma ta kan zolayesu a kan cewa za ta ƙara miji na uku.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel