Alkalin da ya yi shari'ar zaben Atiku da Buhari ya samu karin girma

Alkalin da ya yi shari'ar zaben Atiku da Buhari ya samu karin girma

- Majalisar kolin Alkalai, NJC ta mika sunayen wasu alkalai ga Shugaba Muhammadu Buhari don yi musu karin girma

- Cikin wadanda aka mika sunayensu har da shugaban kotun sauraron karar zaben shugaban kasa Mai sharia Mohammed L. Garba

- NJC ta tantance sunayen alkalan da za a yi wa karin girman ne a taron da ta yi a ranakun 11 da 12 na Agusta kamar yadda kakakin ta Soji Oye ya sanar

Shugaban Kotun Sauraron Karar Zaben Shugaban Kasa (PEPT) da ta tabbatar da nasarar Shugaba Muhammadu Buhari a karo na biyu, Mai Sharia Mohammed L. Garba ya samu karin girma zuwa alkalin kotun koli.

Mai shari'a Garba wanda ya fito daga yankin Arewa maso Yamma wanda a yanzu alkali ne a kotun daukaka kara yana daya daga cikin alkalai hudu da Majalisar Kolin Alkalai, NJC, ta mika sunansu don nada su alkalan kotun koli.

Alkalin da ya yi shari'a zaben Buhari da Atiku ya samu karin girma
Shugaba Muhammadu Buhari. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

Sauran alkalan uku sun hada da Mai sharia Tijjani Abubakar daga Arewa maso Gabas, Mai sharia Abdu Aboki daga Arewa maso Yamma da kuma Mohammed M. Saulawa daga Arewa ta Yamma.

Har wa yau, NJC din cikin sanarwar da mai magana da yawunta, Soji Oye ya fitar ta mika sunayen wasu 18 da ta ke son a nada a matsayin alkalan wasu kotunan.

DUBA WANNAN: Adama Indimi da mijinta sun ziyarci surukinta a fadarsa da ke Kogi (Hotuna)

Wadanda aka mika sunayensu sun hada da Mai sharia Gumna Kashim Kaigama, a matsayin babban alkalin jihar Yobe; Kadi Muhammed Abubakar, a matsayin Grand Khadi na kotun shari'a ta daukaka kara na jihar Katsina da Mai sharia Mathew Emeka Njoku, shugaban kotun daukaka kara ta gargajiya a jihar Imo.

Kazalika, NJC ta mika sunayen wasu alkalai shida da ta ke so a nada a matsayin alkalan manyan kotunan jihar Kano.

Sun hada da Jamilu Shehu Suleiman, Maryam Ahmen Sabo, Sanusi Ado Ma’aji, Abdu Maiwada Abubakar, Zuwaira Yusuf da Hafsat Yahaya Sani.

Majalisar ta NJC ta kuma bada sunayen Clara Jummai Kataps da Kazera Blessing Kodiya da za a nada a matsayin alkalan manyan kotunan jihar Taraba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel