Mun kashe N920m kan annobar cutar Korona a Katsina - Gwamnatin Masari

Mun kashe N920m kan annobar cutar Korona a Katsina - Gwamnatin Masari

Kwamitin yaki da cutar Coronavirus a jihar Katsina ta ce ta kashe kudi milyan 920 cikin bilyan 1 da ta samu na gudunmuwan annobar da ta addabi kasar da duniya gaba daya.

Shugaban kwamitin wanda shine mataimakin gwamnan jihar, Mannir Yakubu, ya bayyana hakan, Daily Trust ta dauko.

Ya ce sun kashe mafi akasarin kudin wajen samar da cibiyoyin killace masu cutar guda uku, gyara dakunan kwanciyan matasa mai gadaje 150 a sansanin horon masu hidiman kasa NYSC, da kuma gyara daki mai gadaje 200 a Batagarawa.

Sauran abubuwan da akayi da kudin sun hada da; samar da cibiyar ajiye masu cutar mai gado 10 a asibitoci 23 dake fadin jihar, sannan taimakawa wajen inganta dakin binciken Sahel medic lab domin zama wajen gwajin cutar.

Yayinda yake magana a taron kaddamar da rabon kayan masarufin rage radadin illar da cutar tayu da gamayyar kamfanoni masu zaman kansu CACOVID suka bada gudunmuwa, Yakubu yace kawo yanzu, an gwada mutane 6,908 a jihar kuma 746 kawai aka samu suna dsuke da cutar.

An samu wafatin mutane 24 yayinda aka sallami 705 kuma akwai saura 17 yanzu, “ Yace.

Ya kara da cewa jihar ta samu kayyakin masurufi 428,311 cikin 469,742 da gamayyar CACOVID ta bada gudunmuwa kuma “ an bamu tabbacin cewa sauran za su iso nan da makonni biyu.”

Mun kashe N920m kan annobar cutar Korona a Katsina - Gwamnatin Masari
Mun kashe N920m kan annobar cutar Korona a Katsina - Gwamnatin Masari
Asali: UGC

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Diyar Buhari, Hanan, za ta auri hadimin minista Fashola

A bangare guda, Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince da fitar da makuden kudi har N8.49 biliyan don siyan manyan kayayyaki 12 na gwajin cutar korona da ta addabi kasar nan.

Za a bai wa hukumar yaki da cutuka masu yaduwa (NCDC) makuden kudin don gwajin cutar, jaridar The Nation ta wallafa.

Ministan lafiya, Osagie Ehanire, ya gabatar da takardar bukatar siyan kayayyakin a madadin hukumar ga 'yan majalisar zartarwar a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

Taron majalisar zartarwar ta samu shugabancin shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidan gwamnati da ke Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel