Kano: Ministan Buhari ya kaddamar da wani katafaren gini da aka kammala a BUK

Kano: Ministan Buhari ya kaddamar da wani katafaren gini da aka kammala a BUK

Ministan ilimi, Adamu Adamu, a ranar Alhamis, ya kaddamar da bude wani katafaren gini na majalisar gudanarwa a jami'ar Bayero (BUK) da ke Kano.

An sakawa katafaren ginin sunan tsohon shugaban jami'ar BUK, Farfesa Adamu Rasheed, wanda yanzu haka shine shugabn hukumar kula da jami'o'in Najeriya (NUC).

Ministan, wanda Farfesa Ishaq Oloyede, shugaban hukumar tsara jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB), ya wakilita ya taya ma'aikata da daliban jami'ar BUK mallakar daya daga cikin manyan gini mafi kyau a jami'o'in Najeriya.

Ya bayyana cewa jami'ar BUK ta na cigaba da samun nasarori ne saboda hadin kan da ake samu a tsakanin shugabanninta na baya da ma su ci a kowanne lokaci.

A cewar ministan, jami'ar BUK ta zama tauraruwa a tsakanin jami'o'in Najeriya. Kazalika, ya yi kira ga sauran jami'o'in Najeriya su yi koyi da BUK.

"Ba zaka taba jin tsohon shugaban jami'ar BUK ya na sukar shugaban da ke kan mulki ba. A jami'ar BUK ne kadai tsofin shugabanni ke hada kai da shugaba mai ci domin ciyar da jami'ar gaba," a cewarsa.

Dangane da sakawa katafaren ginin sunan tsohon shugaban jami'ar BUK, ministan ya ce hakan babbar dabara ce musamman idan aka yi la'akari da irin girman gudunmawar da ya bayar wajen kawo cigaba a jami'ar lokacin shugabancinsa.

Kano: Ministan Buhari ya kaddamar da wani katafaren gini da aka kammala a BUK
Katafaren ginin 'Senate Building' da aka kammala a BUK
Asali: Twitter

Farfesa Rasheed ne ya fara aikin ginin katafaren 'Senate Building' a BUK, sannan shugaban da ya gajeshi, Farfesa Muhammad Yahuza Bello, ya kammala aikin ginin bayan shekara biyar.

DUBA WANNAN: Zargin gwamna da shugabancin Boko Haram: An hukunta gidan radiyon da su ka yada hirar Mailafia

Yahuza, Farfesan lissafi, zai kammala wa'adinsa a matsayin shugaban jami'ar BUK a karshen watan Agusta da mu ke ciki.

Tuni an gudanar da zaben sabon shugaban jami'ar BUK inda Farfesa Sagir Abbas Hassan ya samu nasarar kayar da sauran abokan takararsa.

Sauran wadanda su ka halarci bikin bude katafaren ginin sun hada da; Farfesa Adamu Rasheed da shugaban kwamitin kula da manyan makarantu a majalisar wakilai, Honarabul Suleiman Goro da sauransu.

Tsofin shugabannin jami'ar BUK, Farfesa Ibrahim Umar da Farfesa Sani Zahraddeen, shugaban BUK mai barin gado; Farfesa Muhammad Yahuza Bello, da mai jiran gado, Farfesa Sagiru Abbas, sun halarci taron.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng