Obaseki ya sha da kyar, an ba shi sarauta a karamar hukumar Oshiomhole
Dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar PDO kuma gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da tawagarsa ta kamfen a ranar Laraba an kai musu hari.
Wasu bata gari ne ko 'yan daba suka tare su a gunduma ta gona da ke Uzairue, karamar hukumar Etsako.
Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole dan asalin yankin ne.
Gwamnan tare da magoya bayansa sun kama hanyar zuwa gunduma ta 10, Apana, Uzairue, a lokacin da 'yan daba suka kutsa cikin tawagar kamfen din su.
Sun hari 'yan kauyen tare da wasu magoya bayansa da suka hadu don karbar bakuncin gwamnan da tawagarsa.
Shigar jami'an tsaro lamarin ne yasa 'yan daban suka tsere bayan musayar ruwan wutar da aka yi da su na minti biyar.
Bayan fatattakar 'yan daban da aka yi, gwamnan da tawagarsa sun shiga yankin, inda jama'a suka dinga nuna farin cikinsu da ganinsa sannan suka ci gaba da kamfen ba tare da wata damuwa ba.
KU KARANTA: Ziyartar Buhari: Gwamnan PDP ya dakatar da masu sarauta 12 a jiharsa
A wannan hali, Ogieneni na Uzairue, mai martaba Alhaji Imonikhe Kadiri Omogbai IV, ya bai wa Obaseki sarauta don jinjina masa a kan yadda yake mayar da kai wurin al'amuran addini a jihar.
Bayan yi masa sarautar, an nada mataimakinsan, Kwamared Philip Shaibu a matsayin 'zabin ubangiji' na jama'ar karamar hukumar Etsako ta jihar Edo.
Yankin ya kunshi kauyuma sama da 20. Sun hada da Jattu, Iyamho, wanda kauyensu Oshiomhole ne, Afowa, Elele, Ogbido, Uluoke, Ayaoghena da Ayua.
Sauran sun hada da: Iyuku, Imeke, Afashio, Iyora, Apana, Imonikhe, Yelwa, Ozor, Ikabigbo, Idatto, Ugbenor, Irekpai da Ayogwiri.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis yayin da Gwamnan ya kai ziyara fadar sarkin a cikin kamfen na PDP a mazabar Edo ta arewa.
Tuni dama shirin da ake tsakanin Obaseki da Oshiomhole ya watse, lamarin da ya kawo fadan cikin gida a jam'iyyar APC.
Gwamna Obaseki ya bar jam'iyyar APC tun bayan da aka hana shi fitowa takara a karkashin inuwar jam'iyyar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng