DHQ ta tura rundunonin tsaro na musamman zuwa kudancin Kaduna

DHQ ta tura rundunonin tsaro na musamman zuwa kudancin Kaduna

Jagoran yada labaran atisayen rundunar soji, Manjo Janar John Enenche, ya ce hedikwatar rundunar tsaro (DHQ) ta tura rundunonin soji na musamman zuwa kudancin jihar Kaduna.

Janar Enenche ya ce an tura rundunonin ne domin kawo karshen kashe-kashen jama'a a yankin tare da tabbatar da tsaro a jihar.

Ya sanar da hakan ne ranar Alhamis yayin gabatar da jawabi a kan aiyukan atisayen rundunar tsaro daga ranar 6 ga wata zuwa 12 ga watan Agusta.

DHQ ta tura rundunonin tsaro na musamman zuwa kudancin Kaduna
DHQ ta tura rundunonin tsaro na musamman zuwa kudancin Kaduna Hoto: Nairametrics
Asali: UGC

A cewarsa, bayanai da alamu na zahiri sun nuna cewa kwalliya na biyan kudin sabulu a yaki da makiyan kasa da rundunar soji ke yi.

"Domin kawo karshen sabbin hare-hare da kisan jama'a a kudancin jihar Kaduna, an fadada atisayen SAFE HAVEN zuwa yankin.

"Bayan hakan, an tura wasu rundunonin soji na musamman zuwa wasu sassa na musamman a yankin.

KU KARANTA KUMA: Nasarori 10 da sojin Najeriya suka samu a kan 'yan bindiga

"Yin hakan zai saukakawa rundunar soji samun bayanai tare da tabbatar dasu cikin gaggawa.

"Mu na kira ga jama'ar da ke zaune a yankin a kan su bawa jami'an tsaro hadin kai ta hanyar basu muhimman bayanai."

A wani labarin kuma, dakarun rundunar sojin Najeriya da ke aiki a karkashin atisayen Ofireshon Safe Haven (OPSH) sun samu nasarar kama wasu manyan 'yan bindiga 8 da ke kai hare-hare a kudancin jihar Kaduna.

Rundunar soji ta sanar da cewa wani dan bindiga guda daya ya mutu yayin musayar wuta da dakarun atisayen OPSH da ke aiki a jihar Filato da wani bangare na jihar Bauchi da Kaduna.

Mutane da dama rahotanni suka sanar da cewa an kashe sakamakon hare-haren da 'yan bindiga ke kaiwa a sassan kudancin jihar Kaduna.

Yayin bajakolin 'yan bindigar, kwamandan runduna ta 7 da ke kudancin jihar Kaduna, Kanal David Nwakonobi, ya ce an kama ma su laifin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da kuma gudanar da bincike ta karkashin kasa.

Daga cikin makaman da aka samu a hannun 'yan bindigar akwai; wasu manyan bindigu na gida guda biyu, kananan bindigu na gida guda biyu, babura guda biyu, alburusai da sauransu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel