An kama mai yi wa ƴan fashi da garkuwa jigilar harsashi a Neja (Hoto)

An kama mai yi wa ƴan fashi da garkuwa jigilar harsashi a Neja (Hoto)

Ƴan sandan jihar Niger sun kama wani direba mai suna Abubakar Adamu bayan an gano harsashin AK47 guda 375 a cikin motarsa.

Mai magana da yawun ƴan sandan, Abiodun Wasiu, ne ya bayyana hakan ga manema labarai inda ya ce an kama Wasiu a Suleja yana tuka wata jar Honda Civic maƙare da harsashi.

Ya shaidawa jami'an ƴan sandan cewa yana aiki ne tare da wata ƙungiyar masu fashi da makami da garkuwa da mutane amma shi aikinsa yi musu jigilar makamai kuma ana biyan shi N150,000.

An kama direba da harsashi 375 a jihar Niger (Hoto)
An kama direba da harsashi 375 a jihar Niger (Hoto)
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: A shirye na ke in ba da rayuwata kamar Mandela, inji Mailafia bayan DSS ta sako shi

"Yayin da muke masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa yana cikin wata tawagar masu fashi da garkuwa da mutane, shi aikinsa yi musu jigilar makamai da bindigu," in ji Abiodun.

Abiodun ya ƙara da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an gama bincike kuma ya ce ana ƙoƙarin gano sauran ƴan tawagar ƴan fashin.

A wani labarin, Gwamnan Benue, Samuel Ortom ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta bawa ƴan Najeriya na gari lasisin mallakar manyan bindigu kamar AK47 a matsayin matakin ƴaki da ƙallubalen tsaro a ƙasar.

Gwamnan ya ce a ɗauki tsauraran matakai da dokoki da suka dace domin hana safarar bindigun ta haramtattun hanya kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Wannan da wasu bukatun duk suna dauke ne cikin batutuwan da gwamnan ya gabatar a wani ƙasida da ya gabatar a ranar Talata yayin wani taron intanet da Cibiyar Shugabanci tare da hadin gwiwar NGF suka hada

A cikin ƙasidar da ya gabatar, Ortom yace ya zama dole gwamnatoci a dukkan matakai su amince cewa rashin tsaro babban barazana ce ga cigaban kasar kuma su dage don dakile ta.

Ya kuma bayar da shawarar a rika bawa hukumomin tsaro isassun kudaden horaswa da zai taimaka musu wurin yaki da rashin tsaro a zamanance.

Gwamnan ya bukaci gwamnatin tarayya ta rungumi tsarin gina wuraren kiwon dabobbi na zamani kuma ya shawarce ta da kafa dokar hana kiwo a fili a kasar.

A cewar sanarwa da babban sakataren yadda labaran gwamnan, Terver Akase ya fitar, Ortom ya kuma bayar da shawarar a inganta darajar ilimi da wayar da kan mutane musamman matasa don hakan zai sa suyi watsi da halaye marasa kyau.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel