Sabon salo: Boko Haram sun fara bai wa kananan yara horo

Sabon salo: Boko Haram sun fara bai wa kananan yara horo

Jami'an tsaron hadin guiwa (MNJTF) sun ce kungiyar ta'addanci na Boko Haram ta fara kirkiro wani tsari na amfani da yara a matsayin sojojinta don dawo da rinjayenta da ya warware a yankin tafkin Chadi.

Shugaban fannin yada labarai na rundunar, Timothy Antigha, ya sanar da hakan ne a wata takardar da ya fitar daga N'Djamena a ranar Alhamis, PR Nigeria ta ruwaito.

Antigha, sojan Najeriya mai mukamin kanal, ya ce sun fara diban yara kanana cewa hakan sabon salo ne bayan yadda mayakan su ke ta mika kansu da makamai ga rundunar soji.

Ya ce wannan bayanin abun takaici ne kuma majiyoyin kwararru da hadin guiwar wasu kungiyoyi masu kishi ne suka gano hakan.

Ya kara da cewa, 'yan ta'addan Boko Haram sun sake tabbatar da wannan ci gaban bayan da suka wallafa hotunan yara sanye da kayan sojoji kuma rike da makamai a sabon bidiyon sallah da suka saki.

Sabon salo: Boko Haram sun fara bai wa kananan yara horo
Sabon salo: Boko Haram sun fara bai wa kananan yara horo Hoto: PR Nigeria
Asali: UGC

Kamar yadda yace, diban yara sojoji abu ne mafi muni da Boko Haram ta fara tun farkon kokarin kafa daularta.

KU KARANTA KUMA: Lukman ya fallasa wani sirri da zagon kasa a jam'iyyar APC

"Tun farko, sun fara da sace yara mata 'yan makaranta saboda su samu matan aure sannan su dinga kashe mutane.

"Wannan ci gaban na diban kananan yara a matsayin sojoji ya biyo bayan matsanancin rashin da suka shiga na dakaru da kuma rikicin shugabanci da ya addabesu.

"Sun mayar da hankali wurin diban yara kanana ne saboda za su fi musu saukin juyawa da kuma dasa musu muguwar akidar fiye da manya.

"Sakamakon wannan al'amarin, MNJTF na kira ga iyaye, shugabannin na addinai da gargajiya, da su zuba ido a kan yaransu don gujewa fadawarsu cikin wannan masifa," yace.

Antigha ya shawarci matasa da su kiyaye duk wasu alkawurra da za a musu na shugabanci ko arziki daga kungiyar.

"Labaran matsanancin talauci da kuma shaidanci duk ana samunsu daga tubabbun mayakan. Sun ce babu wani abun a zo a gani da suke da shi balle su bai wa wasu.

"Idan za a tuna, taron kungiyar majalisar dinkin duniya a kan harkokin yara ta hana saka yara cikin rikici ko amfani da su a yayin tarzoma.

"Wannan ne yasa MNJTF ke janyo hankalin majalisar dinkin duniya, cibiyoyin da ya dace da kuma sauran masu ruwa da tsaki da su san abinda ke faruwa kuma a dauka matakan da ya dace.

"A bangarenmu, MNJTF za a ta ci gaba da mayar da hankali wurin bada kariya ga yara da sauran kungiyoyin da ke yankin," ya kara da cewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel