Ku daina kushemu, muna iyakar kokarinmu - DSS ga 'yan Najeriya

Ku daina kushemu, muna iyakar kokarinmu - DSS ga 'yan Najeriya

- Hukumar jami'an tsaro ta farin kaya ta yi kira ga 'yan Najeriya da su dinga basu goyon baya dari bisa dari

- Daraktan hukumar, Yusuf Bichi, wanda ya samu wakilcin Peter Afunanya, ya ce suna aiki tukuru amma 'yan Najerya basu gani

- Ya ce suna bukatar addu'o'i, goyon baya da bayanai daga 'yan Najeriya a maimakon kushe da caccaka

Hukumar jami'an tsaro ta farin kaya, ta yi kira ga 'yan Najeriya da su basu goyon bayan da ya kamata.

Yusuf Bichi, darakta janar na 'yan sandan sirrin, ya yi wannan kiran ne a ranar bikin matasa na duniya ta 2020 wacce hukumar matasa ta Najeriya a Abuja ta shirya.

Bichi ya samu wakilcin Peter Afunanya, kakakin hukumar, ya ce jami'an tsaron farin kayan na iyakar kokarinsu wurin shawo kan manyan kalubale.

Ya ce hukumar tsaron farin kaya tana mayar da hankali wurin "Tabbatar da cewa 'yan kasa sun yi kasuwanci halastacce kuma sun yi rayuwa cike da kwanciyar hankali wurin cikar burikansu."

Ya ce abinda jami'an tsaron farin kayan ke bukata shine goyon baya daga 'yan Najeriya a maimakon kushe.

"Babu kyau a ce matasa, iyaye mata da dukkan 'yan kasa za su ci gaba da kushe hukumomin tsaro," yace.

“Suna matukar kokari, basu bacci, cikin ruwa ko rana. Wani wanda aka kashe a Borno ko wani wuri, mahaifin wani ne, mijin wata mata ne kuma kawun wani ne.

“A don haka ba a murnar mutuwar kowa saboda wani dalili. Suna cikin wani hali mai cike da kalubale.

"Muna aiki babu dare, babu rana. Don haka muna bukatar goyon bayan 'yan Najeriya. Muna bukatar addu'a, muna bukatar bayanai daga wurinku. Duk wanda abun ya shafa akwai bukatar ya bude baki ya yi magana," ya kara da cewa.

Ku daina kushemu, muna iyakar kokarinmu - DSS ga 'yan Najeriya
Ku daina kushemu, muna iyakar kokarinmu - DSS ga 'yan Najeriya. Hoto daga The Cable
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Sakamakon binciken mu a kan hadimin Ganduje, Ali Baba - Rimin Gado

A wani labari na daban, tsohon mai magana da yawun shugaban kasa, Reno Omokri, ya yi martani a kan rahoton hukumar jami'an tsaro ta farin kaya na gayyatar tsohon mataimakin shugaban bankin Najeriya, Obadiah Mailafiya, a kan ikirarin cewa wani gwamnan arewa ne kwamandan Boko Haram.

A wallafar da ya yi a shafinsa na Twitter, Reno Omokri ya ce kamata yayi hukumar jami'an tsaro ta farin kaya ta gayyaci Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna.

Kamar yadda yace, "Duk wanda yake tunanin Obadiah Mailafia yana terere ne, toh ya duba wasu kanun labarai daga 2012 da 2014.

"Mailafia ba wani abu yake cewa ba da makiyaya da kuma 'yan Boko Haram basu cewa. Wannan ne yasa Muhammadu Buhari ke sako tubabbun 'yan Boko Haram tare da yi musu gata.

"Gwamna Nasir El-Rufai ya amsa biyan makiyaya masu kisa a Kaduna ta kudu don su daina kashe-kashe."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel