COVID-19: Sabon dakin jinyar NCDC na Abuja bai fara aiki ba saboda rashin kayan aiki

COVID-19: Sabon dakin jinyar NCDC na Abuja bai fara aiki ba saboda rashin kayan aiki

Duk da fama da ake yi da karancin gadajen jinya a garin Abuja, har yanzu gwamnatin tarayya ta gaza kaddamar da sabon dakin jinya da ta fara ginawa tun kwanaki.

Jaridar Punch ta fahimci dakunan da aka gina na musamman domin killace masu Coronavirus a babban birnin tarayya Abuja bai soma aiki ba har yanzu da mu ke magana.

Bayanan da aka samu daga shafin hukumar NCDC mai takaita yaduwar cuta a ranar Laraba sun nuna a Abuja ne ake da mafi yawan masu COVID-19 da su ke jinya a yanzu.

A garin na Abuja akwai mutane fiye da 3, 170 da su ke kwance su na fama da Coronavirus.

Punch ta ce ana amfani da dakunan da ke cikin manyan asibitoci irinsu babban asibitin Asokoro, da sashen hadura da larurar gaggawa na asibitin Gwagwalada ne wajen jinya.

Watanni shida kenan da su ka wuce da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya koka da cewa NCDC ba ta kammala ginin da ta ke yi a asibitin koyon aiki na UATH ba.

KU KARANTA: NCDC: An samu sababbin mutane 450 da k dauke da COVID-19 jiya

COVID-19: Sabon dakin jinyar NCDC na Abuja ba ya aiki saboda rashin kayan aiki
An garkame dakunan jinyar ciwon Coronavirus a Garin Abuja
Asali: UGC

Daga wannan lokaci zuwa yanzu an iya kammala aikin amma ba a kai ga fara daukar marasa lafiya ba. Abin da ya jawo wannan shi ne babu kayan aiki a cikin wannan wuri.

Da manema labarai su ka ziyarci wannan sabon wuri, sun ga cewa an kai wutar lantarki, amma kofofin wurin duk su na rufe, sannan kuma ba a gama aiki a dakunan bincike ba.

Wani ma’aikaci ya shaidawa ‘yan jarida cewa hukumar REA ba ta dade da jawo wutan lantarki zuwa wurin ba, wanda a cewarsa wannan ne ya jawo aka bata lokaci.

Jami’in ya ce an kai ga zuba kayan zama da na aiki, abin da kurum ya rage shi ne a hada dakin da za a rika gudanar da bincike, daga nan NCDC za ta damkawa UATH ginin.

Wani malamin lafiya ya koka da wahalan da ake sha a sauran wuraren da ake kwantar da masu COVID-19 a asibitocin gwamnati, ya ce akwai bukatar a kammala wannan aiki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel