A shirye na ke in ba da rayuwata kamar Mandela, inji Mailafia bayan DSS ta sako shi

A shirye na ke in ba da rayuwata kamar Mandela, inji Mailafia bayan DSS ta sako shi

Obadiah Mailafia, tsohon mataimakin shugaban babban bankin Najeriya, CBN, ya ce a shirye ya ke ya sadaukar da ransa saboda ƙasarsa kamar tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Nelson Mandela.

An yanke wa, Mandela, ɗan gwagwarmayar yaƙi da banbancin launin fatar hukuncin daurin rai da rai a 1962 amma daga bisani aka salo shi bayan shekaru 27.

Ƴan Sandan Farar Hula, DSS, sun gayyaci Mailafia ne bayan ikirarin da ya yi na cewa daya daga cikin gwamnonin jihohin Arewa ne kwamandan Boko Haram.

A shirye na ke in sadaukar da rayuwata kamar Mandela, inji Mailafia bayan DSS sun sako shi
A shirye na ke in sadaukar da rayuwata kamar Mandela, inji Mailafia bayan DSS sun sako shi
Asali: Twitter

Mailafia ya yi wannan ikirarin ne cikin wata hira da aka yi da shi a wani gidan rediyo da ke Abuja a ranar Litinin.

Rahotanni sun ce ya isa ofishin na DSS da ke Jos misalin ƙarfe 12.48 na rana tare da lauyoyinsa Pius Akubo mai muƙamin SAN da Yakubu Bawa.

DUBA WANNAN: Miji ya kashe kansa saboda matarsa ta ƙi bari ya kusance ta watanni 22 bayan aurensu

Ɗaruruwan magoya bayansa sun yi tattaki zuwa ofishin na DSS a kuba road dauke da takardu masu ɗauke da rubutun cewa ba za su tafi ba har sai an sako shi.

Magoya bayansa sun tsaya a wajen ofishin na DSS har zuwa karfe 6.30 na yamma da aka sako shi.

Da ya ke yi wa magoya bayansa jawabi, Mailafia ya ce yana nan kan bakansa game da abinda ya faɗa yayin hirar da aka yi da shi a gidan rediyon.

A shirye na ke in sadaukar da rayuwata kamar Mandela, inji Mailafia bayan DSS sun sako shi
A shirye na ke in sadaukar da rayuwata kamar Mandela, inji Mailafia bayan DSS sun sako shi
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa an masa tarba mai kyau a ofishin na DSS, inda ya ƙara da cewa wasu sun yi wa kalamansa gurguwar fahimta.

Ya ce ba zai sauya abinda ya faɗa ba domin a matsayinsa na mai faɗa aji akwai wasu bayanai da zai iya sani da ba dole ne kowa ya sani ba.

Mailafia ya ce bai tabbatar da abinda majiyarsa ya faɗa masa ba saboda babu yadda za ayi ya bi su zuwa sansanin su ya tabbatar da cewa gwamnan arewan ne kwamandan su.

Ya kuma ce shi mutum ne mai son zaman lafiya kamar yadda sunansa ya kunsa saboda haka ba neman tayar da rikici ya ke yi ba sai dai ƙauna da kishin ƙasarsa da ya ke yi.

Wani sashi na cikin jawabin da ya yi; "Hakkin gwamnati ne kiyayye rayuka da duniyoyin al'ummar ta da yara. Wannan babban batu ne. Duk yaron da aka kashe ji na ke kamar nawa ne.

"Ina ƙaunar Najeriya. Kamar Mandela a shirye na ke in sadaukar da rayuwa ta saboda Najeriya idan buƙatar hakan ya tashi."

Mailafia ya yi wa hukumar tsaron godiya bisa tarbar da tayi masa kuma ya yi addu'ar Allah ya kawo zaman lafiya a Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel