Buhari ya yi ta'aziyar rasuwar Walter Carrington

Buhari ya yi ta'aziyar rasuwar Walter Carrington

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi taaziyar rasuwar tsohon jakadan kasar Amurka a Najeriya, Walter Carrington kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Shugaban kasar cikin sanarwar da kakakinsa, Mallam Garba Shehu ya fitar ya ce bayyana Carrington a matsayin "tsohon abokin Najeriya kuma kwararre da jarumin jakada."

A cikin sakon taaziyar da ya fitar a yammacin Laraba, Buhari ya yabi tsohon jakadan wanda ya ce, "ya goyi bayan mutanen Najeriya a filli a lokacin da suka yi fafutikan komawa demokradiyya bayan soke zaben 12 ga watan Yunin 1993 da marigayi Moshood Abiola ya lashe."

Buhari ya yi ta'aziyar Walter Carrington
Buhari ya yi ta'aziyar Walter Carrington
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Miji ya kashe kansa saboda matarsa ta ƙi bari ya kusance ta watanni 22 bayan aurensu

Buhari ya ce labarin demokradiyyar Najeriya karkashin jamhuriyya ta hudu ba za ta taba cika ba ba tare da an ambacii jarumai irinsu Ambasada Carrington.

"A madadin iyalai na, gwamnati da al'ummar Najeriya, Ina mika taaziya ta ga iyalan mamacin, abokansa, masu goyon bayansa da gwamnati da al'ummar kasar Amurka," in ji shi.

A wani labarin, kun ji cewa Allah ya yi wa shugaban karamar hukumar Onigbongbo a Legas, Mr Babatunde Oke rasuwa.

Ya rasu ne a safiyar yau Laraba 12 ga watan Agusta sakamakon cutar COVID-19 wacce aka fi sani da korona kamar yadda PM News Nigeria ta ruwaito.

A cewar sakon da aka wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta ta Facebook, Oke ya rasu a yau a asibitin St. Nicholas da ke Legas Island inda aka mayar da shi lokacin da ciwon ya yi tsanani.

Da farko ana kula da shi ne a cibiyar killace masu korona da ke Gbagada. Oke yana kan waadin mulkinsa na biyu a matsayin shugaban karamar hukuma.

Shine shugaban karamar hukuma na biyu da annobar korona ta yi ajalinsa a jihar Legas.

A watan Yuni, shugaban karamar hukumar Agbado/Oke-Odo LCDA, Augustine Adeoye Arogundade shima ya mutu sakamakon kamuwa da cutar da COVID-19.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel