Ina so in kwashe shekaru 90 kacal a duniya - Gwamna Ortom

Ina so in kwashe shekaru 90 kacal a duniya - Gwamna Ortom

Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom, a ranar Laraba, 12 ga watan Agusta, ya ce idan Ubangiji ya bashi dama, yana son kwashe shekaru 90 kacal ne a duniya.

Gwamnan zai cika shekaru 60 a duniya a 2021, jaridar The Nation ta ruwaito.

A yayin zantawa da wata kungiyar matasa don tunawa da ranar matasa ta duniya a ranar Laraba, Ortom ya nuna damuwarsa a kan matsalolin da suka addabi kasar nan da duniya baki daya.

Gwamnan ya bayyana yaki da rashawa da gwamnatin tarayya ke yi a matsayin zabe da son ganin bayan wasu.

Ina so in kwashe shekaru 90 kacal a duniya - Gwamna Ortom
Ina so in kwashe shekaru 90 kacal a duniya - Gwamna Ortom Hoto: Channels TV
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun kama tsohon da ya sace yarinya yana bada haya don lalata da ita

"Mutanen da suka saci kaza ne ake wurgawa gidan yari amma masu satar biliyoyi suna yawo hankali kwance."

A bangaren matasa, ya ce matasa na bukatar a wayar musu da kai a kan yadda za su yi amfani da lokacinsu a kafafen sada zumuntar zamani da kuma gujewa zagin manya.

"Babu wanda zai biya ku don kun zagi na gaba da ku a Facebook amma za ku iya amfani da kafar don samar da mafita gareku ba zagi ba."

Ya jaddada kiransa ga gwamnatin tarayya da ta bar 'yan kasa nagari masu hankali su dinga yawo da makamai kamarsu AK 47 kamar yadda miyagu ke yi suna kashe mutane.

"Me yasa za su bada lasisi amfani da bindigar toka yayin da wadanda ke zuwa kashemu suna amfani da AK 47," Ortom ya tuhuma.

Sai dai ya ce ya kamata a bi tsarin doka sosai wajen aiwatar da wannan manufar domin gujewa shigar makaman hannun wadanda bai dace ba.

Gwamnan ya ce ya zama dole gwamnati a dukkan mataki su saka hannu wurin yakar rashin tsaro da ya zama babban kalubale a kasar.

Ya sake bayyana cewa, akwai bukatar a sakarwa hukumomin tsaro kudi da kuma horar da jami'an tsaron don yakar rashin tsaron.

Gwamnan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta rungumi sabbin tsarin ilimi wanda zai kara wayar wa da jama'a kai.

Gwamna Ortom ya bada shawara a kan diban ma'aikatan tare da samar wa matasa wurin aiki don su bar kan titi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel