Bidiyo: NAF ta lalata cibiyar sufurin kungiyar Boko Haram, an kashe dumbin mayaka

Bidiyo: NAF ta lalata cibiyar sufurin kungiyar Boko Haram, an kashe dumbin mayaka

Dakarun rundunar sojin sama da ke aiki a karkashin rundunar atisayen LAFIYA DOLE sun yi ruwan wuta a wata cibiyar adana sufurin 'yan Boko Haram tare da kashe dumbin mayakan kungiyar.

A cikin wata sanarwa da rundunar soji ta fitar a shafinta na yada labarai, ta bayyana cewa dakarun NAF sun kai hari ranar Talata a kan cibiyar da ke Yamud a yankin Gulumba Gana - Kumshe a jihar Borno.

Sanarwar ta bayyana cewa dakarun NAF sun kai harin ne bayan samun sahihan bayanan sirri a kan cewa cibiyar na daya daga cikin manyan cibiyoyin da mayakan kungiyar Boko Haram ke adana kayan sufuri.

Kazalika, sanarwar ta kara da cewa rundunar soji ta tabbatar da hakan, sannan ta gano cewa mayakan kungiyar Boko Haram kan tattaru a cibiyar domin tsara yadda za su kaddamar da hari da kuma kayan sufurin da su ke bukata.

Rundunar soji ta bayyana cewa samamen dakarun NAF ta sararin samaniya ya gano wasu gine-gine a yankin da mayakan kungiyar Boko Haram ke amfani da su domin adana kayansu da kuma yin taro.

Manjo Janar John Enenche, jagoran sashen yada labaran rundunar tsaro, ya sanar da cewa an lalata dukkan gine-ginen da 'yan Boko Haram ke amfani da su domin ajiya da kuma gudanar da taro.

Kazalika, ya kara da cewa an kashe mayakan kungiyar Boko Haram ma su dumbin yawa yayin luguden wuta da dakarun NAF su ka yi.

DUBA WANNAN: Yadda manyan jami'an soji suka watsar da yaki suka koma kiwon kifi da tsuntsaye a Borno

A jiya, Talata, ne Legit.ng ta wallafa rahoton cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya tuhumi shuwagabannin hukumomi da rundunonin tsaro kan yadda 'yan ta'adda ke samun makamai duk da cewa ya rufe bodar kasar.

Da yake jawabi a taron gwamnonin jihohi da shuwagabannin tsaro a ranar Talata a Abuja, Buhari ya nuna damuwarsa kan yadda 'yan ta'addan ke samun makaman da suke ta'addanci a kasar.

Bidiyo: NAF ta lalata cibiyar sufurin kungiyar Boko Haram, an kashe dumbin mayaka
Jirgin yakin rundunar NAF
Asali: Twitter

"Wadannan 'yan ta'addan suna rayuwa a cikin kauyuka. Amma me yasa makamansu basa karewa?" ya tuhumi shuwagabannin hukumomin tsaro da hafsoshin rundunar soji.

Taron ya kare da yin kira kan samar da dabaru na kawo karshen ta'addanci farat daya, yayin da jami'an tsaro zasu mayar da hankali wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Taron ya mayar da hankali kan matsalolin tsaro da yadda za a shawo kansu, inda aka nuna muhimmancin killace bayanan sirri domin karya lagon 'yan ta'addan.

Mahalarta taron sun nuna yakininsu na cewar idan aka sake samun yarda tsakanin jami'an tsaro da mutanen gari, to za a samu nasara wajen tattara bayanan sirri mai yawa kan 'yan ta'addan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel