Mu shugabancin kasa muke so a 2023 ba Biyafara ba - Ohanaeze Ndigbo

Mu shugabancin kasa muke so a 2023 ba Biyafara ba - Ohanaeze Ndigbo

Kungiyar yan kabilar Igbo a Najeriya, Ohanaeze NdIgbo ta bayyana cewa shugabanci kasa kawai take sha'awa ba ballewa daga Najeriya ba da wasu ke ta ikirari.

Kungiyar ta jaddada cewa lallai shugabancin kasa a 2023 hakki ne yan yankin kudu maso gabas, ba alfarma ba.

Shugaban kungiyar Ohaneze NdiIgbo, shiyar jihar Anambara, Cif Damian Okeke-Ogene, ya bayyana hakan yayinda yake hira da manema labarai a taron kungiyar da sukayi.

Ya ce shugabannin kungiyar basu baiwa kowani mutum ko kungiyar aikin neman ballewa daga Najeriya ba amma kawai shugaban kasa dan kabilar Igbo suke so a 2023.

Ya ce wasu matasan yankin dake ikirarin yakin neman kafa kasar Biyafara na yi ne saboda irin zalunci da bangarancin da ake nunawa al'ummar Igbo.

A cewar Okeke-Ogene: "Muna neman shugaban kasa Igbo saboda shugabancin Ohanaeze Ndigbo karkashin jagorancin Nnia Nwodo na da hakkin neman kujerar shugabancin Najeriya."

"Ba shi da hakkin ballewa da neman yancin Biyafara. Shi yasa muke cewa a bamu abinda ya zama hakkinsu kuma shugaban kasa dan kabilar Igbo muke nema."

"Game da matasan IPOB, yaranmu ne kuma suna hakan ne don sun lura Najeriya bata shirya basu abinda suke so ba."

"Idan suka amince Najeriya zata bamu abinda muke so, nayi imanin zasu natsu. Najeriya tamu ce gaba daya."

Ya lashi takobin cewa yan kabilar Igbo ba zasu daina gwagwarmaya ba sai sun samu shugabancin kasar nan.

Mu shugabancin kasa muke so a 2023 ba Biyafara ba - Ohanaeze Ndigbo
Mu shugabancin kasa muke so a 2023 ba Biyafara ba - Ohanaeze Ndigbo
Asali: UGC

A makon jiya, Tsohon shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Okwesilieze Nwodo, ya ce idan ba'a baiwa kabilar Igbo shugabancin kasa a 2023 ba, masu arzikin kudu maso yamma zasu hada kai da shugaban kungiyar yakin neman Biyafara IPOB, Nnamdi Kanu wajen ballewa daga Najeriya.

A hirar Okwesilieze Nwodo da jaridar Vanguard, ya jinjinawa Tanko Yakassai, bisa kiran da yayi a baiwa Igbo shugabancin kasa a 2023.

Ya ce shekaru 50 kenan ana cin zarafin Igbo, kuma ya shawarci dukkan masu son rana goben yaransu yayi kyau su zabi Igbo a 2023.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel