SEMA ta yi wa kananan hukumomin Kano 20 gargadi game da ambaliyar ruwa

SEMA ta yi wa kananan hukumomin Kano 20 gargadi game da ambaliyar ruwa

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano, SEMA, ta gargadi mazauna wasu kananan hukumomi a kalla 20 a jihar su tsaftace magudanan ruwansu domin kare afkuwar ambaliyar ruwa.

Babban sakataren hukumar, Dr Sale Jili ne ya yi wannan gargadin a wata hira da ya yi da manema labarai a ranar Laraba kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Jili ya ce kananan hukumomin da abin ka iya shafa ya sun hada da Kabo; Gezawa, Bebeji, Kura, Gwarzo, Shanono, Wudil da Gaya.

SEMA ta yi wa kananan hukumomin Kano 20 gargadi game da ambaliyar ruwa
SEMA ta yi wa kananan hukumomin Kano 20 gargadi game da ambaliyar ruwa
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Buhari ya kwatanta mayakan Boko Haram da "mayunwata masu nema abinci"

Sauran sun sune Gabasawa; Danbatta, Bagwai, Rimin Gado, Ungogo, Gwale, Fagge, Tarauani, Nasarawa, Dala, Kumbotso da Kano Municipal.

A cewarsa, wannan gargadin ta zama dole bayan hasashen da hukumar nazarin yanayi, NiMeT, ta yi inda ta lissafa jihohin da za su iya fuskantar ambaliyar ruwa a 2020 saboda ruwan sama mai yawa ciki har da Kano.

"Abinda muke son tabbatarwa shine bude magudanai domin ruwa ya rika wucewa," in ji shi.

Jili ya ce wasu gidajen da laka aka gina su yayin da wasu kuma bulo din da aka gina su ba masu kwari bane don haka akwai yiwuwar ruwan sama mai yawa ya zubar da ginin.

Ya bayar da tabbacin cewa hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin aikin ta na kare rayuka da dukiyoyin mutane.

Jili ya ce, "Za mu yi hadin gwiwa da sarakuna biyar na jihar da hakimai domin wayar da kan mutane muhimmancin tsaftace muhalli don kiyayye ambaliyar ruwa da iska mai karfi.

"Ina kira ga wadanda ambaliyar ruwa bai shafa ba su dauki matakan kiyayye kansu ta hanyar tsaftace magudanen ruwa da zubar da shara a wurin da suka dace."

Sakataren ya kuma roki shugabannin addini da malamai su taya jihar da addua domin Allah ya kare afkuwar iftila'in.

Kazalika, hukumar ta ce ruwan sama ya lalata tsirai a gonaki da kudinsu ya kai Naira miliyan 4O a karamar hukumar Bagwai.

Sakataren hukumar ya bayyana cewa abin ya shafi manoma 55O a garuruwan Gadanya, Jobar, Jobe, Gadawa da Galawa.

Ya ce hukumar tana iya kokarin ta domin tallafawa manoman.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: