An sake yin rashin shugaban karamar hukuma a Legas
Allah ya yi wa shugaban karamar hukumar Onigbongbo a Legas, Mr Babatunde Oke rasuwa.
Ya rasu ne a safiyar yau Laraba 12 ga watan Agusta sakamakon cutar COVID-19 wacce aka fi sani da korona kamar yadda PM News Nigeria ta ruwaito.
A cewar sakon da aka wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta ta Facebook, Oke ya rasu a yau a asibitin St. Nicholas da ke Legas Island inda aka mayar da shi lokacin da ciwon ya yi tsanani.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Buhari ya nada Adamu Adaji a matsayin shugaban hukumar NBC
Da farko ana kula da shi ne a cibiyar killace masu korona da ke Gbagada.
Oke yana kan waadin mulkinsa na biyu a matsayin shugaban karamar hukuma.
Shine shugaban karamar hukuma na biyu da annobar korona ta yi ajalinsa a jihar Legas.
A watan Yuni, shugaban karamar hukumar Agbado/Oke-Odo LCDA, Augustine Adeoye Arogundade shima ya mutu sakamakon kamuwa da cutar da COVID-19.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng