Da duminsa: Kano ta nada sabbin alkalai 6 na babbar kotu (Sunaye)

Da duminsa: Kano ta nada sabbin alkalai 6 na babbar kotu (Sunaye)

- Majalisar sharia'a ta kasa ta aminta da nadin sabbin alkalai 6 na babban kotu a jihar Kano

- Bayani game da hakan na kunshe ne a wata takarda da Baba Jibo, kakakin hukumar ya fitar

- Ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta aminta da nadin ne a ranar 11 ga watan Augustan 2020

Majalisar shari'a ta kasa ta amince da nadin sabbin alkalai 6 na babban kotu a jihar Kano. Wannan na kunshe ne a wata takarda da kakakin hukumar, Baba Jibo, ya fitar.

Takardar ta ce gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da nadi a ranar Talata, 11 ga watan Augustan 2020 bayan bin tsarin da ya dace wurin nadin.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, sabbin alkalan babbar kotun sun hada da:

1. Mai sharai'a Jamilu Shehu Sulaiman

2. Mai shari'a Zuwaira Yusuf

3. Mai shari'a Maryam Sabo

4. Mai shari'a Abdu Maiwada Abubakar

5. Mai shari'a Sunusi Ma'aji

6. Mai shari'a Hafsat Yahaya Sani

Da duminsa: Kano ta nada sabbin alkalai 6 na babbar kotu (Sunaye)
Da duminsa: Kano ta nada sabbin alkalai 6 na babbar kotu (Sunaye). Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dole in mayar da Obasanjo gidan fursuna idan na hau shugabancin kasa - Fayose

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya yi kira ga sarkin Kano, Aminu Ado-Bayero, da ya yi amfani da kujerarsa wurin assasa hadin kai na yankin arewacin kasar nan.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne ga sarkin yayin da ya kai ziyara gidan gwamnatin jihar a ranar sati, kamar yadda yake kunshe a wata takarda da mai bada shawara na musamman a kan fannin yada labarai ga gwamnan, Zailani Bappa, ya fitar.

Matawalle ya jaddada cewa arewa na matukar bukatar shugabanni da za su hada kan jama'a don komawa saiti daya na siyasa da al'adu.

"Mai martaba, arewa na bukatar shugabanninsu da za su hada kan jama'arta a siyasance da al'adance kamar baya," Matawalle ya ce.

Gwamnan ya danganta rashin hadin kan yankin da ci gaban rashin ganin girman sarakunan gargajiya.

Ya tuna cewa, a baya jama'a suna mutunta masarautun gargajiya a kan yadda suke bada gudumawa wurin hadin kan al'umma da zaman lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel