Zaben Ondo: APC ta nada Sanwo Olu shugaban kwamitin yakin neman zabe

Zaben Ondo: APC ta nada Sanwo Olu shugaban kwamitin yakin neman zabe

Shugaban riko na jam’iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, ya bayyana sunayen mambobin kwamitin mutum 104 da za su ja ragamar yakin neman zaben gwamnan jihar Ondo.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamitin zartaswa na jam’iyyar APC ya fitar a ranar Talata da daddare.

Sanarwa ta bayyana cewa, Gwamna Babajide Sanwo Olu na jihar Legas, shi ne zai jagoranci kwamitin yakin neman zaben gwamnan Ondo da za a gudanar a ranar 10 ga watan Oktoba.

Gwamnan jihar Ondo mai ci a yanzu, Rotimi Akeredolu, shi ne marikin tutar jam’iyyar da ke neman sake samun nasarar riko da akalar jagorancin jihar.

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe; Shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe; Shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC
Asali: Original

Sauran jam’iyyun adawa da Akeredolu zai fafata da su sun hadar da PDP da ZLP (Zenith Labour Party) wadda dan takararta ya kasance mataimakin gwamnan, Agboola Ajayi.

Kwamitin yakin neman zaben na APC ya kunshi gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalung, a matsayin mataimakin jagora da kuma Mustapha Salihu a matsayin sakatare.

KARANTA KUMA: Covid-19: Badaru ya rarraba kayan abinci ga magidanta 40,000 a Jigawa

Daga cikin ‘yan kwamitin akwai gwamnonin APC takwas, fiye da tsoffi da ‘yan majalisar tarayya masu ci guda arba’in, ministoci da sauransu.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, a na sa ran za a rantsar da kwamitin yakin neman zaben ranar Asabar a hedikwatar jam’iyyar APC da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Ga jerin sunayen 'yan kwamitin APC 104 da za su ja ragamar yakin neman zaben gwamnan Ondo:

1. Babajide Sanwoolu (Shugaba)

2. Simon Lalong (Mataimaki)

3. Rt. (Hon.) Femi Gbajabiamila

4. Sanata Ovie Omo-Agege

5. Gbenga Isiaka Oyetola

6. Dapo Abiodun

7. Kayode Fayemi

8. Abubakar Badaru

9. Mallam Nasir El-rufai

10. Babagana Zulum

11. Sanata George Akume

12. Sanata Aliyu Wammako

13. Abdulazeez Yari

14. Muhammed Bindow Jibrilla

15. Rt. (Hon.) Yakubu Dogara

16. M. A Abubakar

17. Rotimi Amaechi

18. Sanata Ibikunle Amosun

19. Ogbeni Rauf Aregbesola

20. Babatunde Raji Fashola

21. Otunba Niyi Adebayo

22. Chief Timipre Sylva

23. Rochas Okorocha

24. Sanata Ajayi Boroffice

25. Mrs. Stella Okotete

26. Barr. Ismail Ahmed

27. Chief Ayiri Emami

28. Dr. Mahmud Halilu (Modi)

29. Hajiya Sadiya Umar Farouq

30. Hon. Aliyu Ugbane

31. Mrs. Kemi Nelson

32. Chief Omotayo Alasoadura

33. Rt. Hon. Abubakar Y. Suleiman (ƊanGaladiman Ningi)

34. Chief Ekechi Emenike

35. Hon. Emeka Nwajuba

36. Senator Osita Izunaso

37. Chief Victor Giadom

38. Garba Maigudu

39. Chief Enyi C. Enyi

40. Hon. Khadija Bukar Abba Ibrahim

41. Sanata Sani Abubakar Danladi

42. Sanata Andy Uba

43. Sanata Olorunminbe Mamora

44. Hassan Kafayos

45. Hon. Gololo

46. Hon. Mailantariki

47. Hon. Abdullahi Bello (USD)

48. Hon. Dakuku Peterside

49. Osita Okechwuku

50. Sen. Ifeanyi Ararume

51. Chief Akin Ricketts

52. Engr. Abdullahi Garba Ramat

53. Senator Jibrin Wowo

54. Alh. Yakubu Saidi

55. Alh. Ubale Hashim

56. Hon. Muhammed Bello Nasarawa

57. Hon. Umar Konto

58. Sen. Abubakar Gieri

59. Sen. Jonathan Zwingina

60. Rt. (Hon.) Nse Ntuen

61. Patrick Akaiso

62. Hon. Bashir Malami Wurno

63. Hon. Muhammed Sani Ibrahim

64. Hon. Farouq Adamu Aliyu

65. Amb. OlusolaIji

66. Hon. Shina Peller

67. Chief Olusola Oke

68. Chief Uche Ogah

69. Hon. Prince Akinremi Alaide

70. Comrade Tony Nwoye

71. Otuekong Nathaniel Uyio

72. Precious Sunday Effiong

73. Prince Ekerendu Esitikot

74. D. O Olusegun

75. Ayo Oyelowo

76. Musa Haro Daura

77. Dr. Usain Kangiwa

78. Engr. (Hon.) Abdullahi Muslim

79. Engr. Sale Danyaro

80. Barr. Bodunde Opeyemi Adam

81. Hon. Motunrayo Akintomide

82. Hon. Gbenleke Olawore

83. Dr. Ahmadu Attai

84. Rt. (Hon.) Emah Bassey

85. Hon. (Prince) Emmanuel Inwang

86. Hon. Akpovoka Efeni Julius

87. Hon. Pam Ishaya Rondong

88. Pastor Bankole Oluwajana

89. Hon. Nelson Alapa

90. Abubakar Sadiq

91. Chief Rita Begho

92. Hon. Hadi Ametuo

93. Barr. Alex Onwudiamu

94. Chief Cosmas Ighoraye

95. Barr. Raymond Guana

96. Hon. Doris Uboh

97. Chief Paulinus Akpeki

98. Chief Claudius Enegesi

99. Mrs. Julie Okah-Donli

100. Chief Dekivie Ikiogha

101. Dr. Hinks Dumbo

102. Hon. Israel Sunny-Goli

103. Patrick Okomiso

104. Comrade Mustapha Salihu (Sakatare)

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel