Miji ya kashe kansa saboda matarsa ta ƙi bari ya kusance ta watanni 22 bayan aurensu

Miji ya kashe kansa saboda matarsa ta ƙi bari ya kusance ta watanni 22 bayan aurensu

An kama wata mata a kasar India bayan mijinta ya kashe kansa a kan ikirarin ba ta taba amince masa sunyi kwanciyar aure ba tun bayan daura musu aure.

An kama Geeta Parmar, mai shekaru 32, mai zaune a Maninagar a Gujarat kan zarginta da hanncu wurin taimaka wa mijinta kashe kansa bayan mahaifiyar mjinta da ya rasu ta yi karar ta.

Muli Parmar, mai shekaru 55, ta yi ikirarin Geeta ba tayi kwanciyar aure da mijinta, Surndrasinh ba yayin zaman auren da su kayi na watanni 22.

Miji ya kashe kansa saboda matarsa ta ki bari ya kusance ta watanni 22 bayan daura aure
Miji ya kashe kansa saboda matarsa ta ki bari ya kusance ta watanni 22 bayan daura aure. Hoto daga Shutterstock/Cindy Hughes
Asali: Twitter

Mahaifiyar marigayin ta ce rashin saduwar ne ya janyo wa danta tsananin damuwa har zaman aurensu ya tabarbare. Ta bayyana cewa ta gano ba su kwana daki daya a lokacin da ta kai musu ziyara.

DUBA WANNAN: Buhari ya kwatanta mayakan Boko Haram da "mayunwata masu nema abinci"

Surndrasinh ya shaidawa ma mahaifiyarsa cewa shi da Geeta ba su taba kwanciyar aure ba kamar yadda rahoton yan sanda ya ce.

Muli ta yi ikirarin cewa Geeta ta yi rantsuwar cewa ba za ta taba saduwa da mijinta ba yayin zaman aurensu.

"Akwai lokacin da na taba shiga dakinsu kuma na gano kowa a gadonsa daban ya ke barci," kamar yadda Muli ta yi ikirari a rahoton yan sanda.

Times of India ta ruwaito cewa ma’auratan sun dade suna rikici a kan lamarin kafin daga bisani Geeta ta kwashe kayanta ta koma gidan iyayen ta.

A ranar 27 ga watan Yuli, wasu daga cikin iyalan Surndrasinh sun dawo kawai sai suka gano ya kashe kansa.

Surndrasinh, maaikacin hukumar kula da jiragen kasa ya auri Geeta, matarsa ta biyu a watan Oktoban shekarar 2018 bayan ya rabu da tsohuwar matarsa shekaru biyu da suka shude.

A halin yanzu rundunar yan sandan kasar ta Shaherkotda a Ahmedabad suna bincike a kan lamarin a Gujarat.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel