A koda yaushe zan kasance mai goyon bayan matasa - Atiku

A koda yaushe zan kasance mai goyon bayan matasa - Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya sake jaddada kyakkyawar alakar da ke tsakaninsa da matasa da kasancewa garkuwar kare martabarsu.

Atiku a ranar Talata ya bai wa matasan Najeriya tabbacin cewa shirye ya ke wajen tsare mutuncinsu da kuma goyon baya a ko da yaushe walau a lokacin tsanani ko sabanin haka.

Furucin Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya zo a yayin bikin cika shekaru 20 ta ranar Matasa na duniya, IYD.

A wani sako da ya rattaba hannu a kai, Wazirin na Adamawa ya nemi Matasa a kan kada su yi kasa a gwiwa a fafutikar da suke yi ta samar da ci gaba mai dorewa a kasar nan.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar
Asali: UGC

Ya ce: “Ina taya dukkanin Matasa a fadin duniya murna yayin bikin cika shekaru 20 da ranar Matasa ta Duniya ta yi.”

“Ba zan gushe ba wajen ci gaba da baku goyon baya da kulawa saboda a matsayinku na matasa, ku ne manyan yanzu kuma manyan gobe.”

“Ina jinjinawa Matasan Najeriya musamman irin kwazonsu, jajircewa da sadaukar da kai da suke yi domin ganin kasar nan ta taka mataki na ci gaba na kololuwa.”

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, taken bikin na bana a takaice shi ne 'zaburar da Matasa da sanya su cikin al’amuran gudanarwa a fadin duniya'.

KARANTA KUMA: Gwamna Matawalle ya ba da umarnin biyan N50,000 ga Dagatai duk wata

“Wannan take ya haskaka muhimmanci na gaske dangane da irin tsinkayen da duniya take yi a kan matasa.”

“Haka kuma wannan take yayi daidai da burin da ke zuciyata kamar yadda na fayyace aniyar sanya kashi 40 cikin 100 na matasa a gwamnatina yayin yakin neman zabe a 2019.”

“Kuma ba zan sauka daga kan wannan kudiri ba.”

“A wannan zamani da duniya take fama da annobar korona, akwai nauyin da ya rataya a wuyansu na kare kawunansu daga kamuwa da cutar.”

“Haka kuma matasa na da hakkin agazawa hukumar dakile yaduwar cututtuka NCDC domin rage yaduwar cutar a kasar.”

“Musamman ta hanyar wanke hannaye, amfani da takunkumin rufe fuska da kauracewa taron jama’a gami da bayar da tazara da yin nesa-nesa da juna.”

“Tabbas rayuwar bil Adama ta dogara ne a kan matasa a yayin da ake bukatar karsashinsu wajen ganin an murkushe wannan annoba.”

“A matsayinku na matasan yau da gobe, ina horonku a kan yayata aminci baka da kuma a aikace; nuna kishin kasa a dukkan matakai.”

“Ku tsarkake kanku da nuna ƙiyayya da kuma fifita ƙwarewar sama da kowane irin ra'ayi.

“Ta hanyar haka ne kadai Najeriya za ta iya kai wa tudun mun tsira inda za mu sharbi romon da muke buri a yanzu.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel