Muna roƙon 'yan Najeriya su ƙara haƙuri kan matsalar rashin tsaro - Buhari

Muna roƙon 'yan Najeriya su ƙara haƙuri kan matsalar rashin tsaro - Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya roki ‘yan Najeriya da su dai kara hakuri kan matsalar rashin tsaro da kasar ke ci gaba da fuskanta a baya bayan nan.

Shugaba Buhari ya ce tabbas gwamnatinsa tana iyaka bakin kokari don ganin ta sayo karin makamai da za su karfafi ayyukan inganta tsaro a kasar.

Wannan sanarwa ta shugaba Buhari ta zo ne cikin wani sako da ya wallafa kan shafinsa a dandalin sada zumunta na Twitter a ranar Litinin, 10 ga watan Agusta.

Cikin sakon da Buhari ya wallafa, ya ce gwamnatinsa tuni ta fitar da kudaden sayo karin makaman yaki, kuma ana tantance wasu a gabar ruwa yayin da kuma ake kera wasu sabbi a yanzu haka.

Shugaba Buhari yayin gana wa da Gwamnonin Arewa maso Gabas
Shugaba Buhari yayin gana wa da Gwamnonin Arewa maso Gabas
Asali: Twitter

“Muna matukar kokara wajen tabbatar da cewa mun inganta harkokin tsaro a wasu sassa na Najeriya wanda daga cikin fadi-tashin da muke yi akwai kashe makudan kudi don sayo makamai,” in ji Buhari.

“Ina rokon ‘yan Najeriya da su kara hakuri kan maganar sayen makamai musamman a wannan lokaci da annobar korona ta yi mummunan tasiri kan kasashen da ke samar da su.”

“Bayan haka da zarar makaman yakin sun iso gare mu, dole sai mun ba wa jami’an tsaro horo a kan iya sarrafa makaman gabanin a soma aiki da su.”

A wani rahoto mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, Shugaban kasa Buhari ya fadi dalilin da ya sanya a gaza kawo karshen tayar da kayar baya a Arewa maso Gabashin Najeriya.

KARANTA KUMA: Dakarun Nijar sun harbe masu kai wa 'yan Boko Haram makamai a kan hanyarsu ta zuwa Najeriya

Buhari ya dora laifin rashin samun nasara a kan yaki da 'yan ta'adda na Boko Haram a Arewa maso Gabashin Najeriya kan rashin isasshen kudi a baitul malin gwamnati.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin ganawarsa da kungiyar Gwamnonin yankin Arewa maso Gabas a fadarsa da ke Aso Villa a birnin Abuja.

Haka kuma shugaban kasar ya kara da cewa cutar korona ce ta yi tasirin gaske wajen kara tsananta lamarin.

Amma ya ce akwai damuwa matuka bisa yadda matsalar tsaro ke kara tsananta fiye da yadda ya samu abin lokacin da ya hau karagar mulki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel