Jiragen ruwa 18 ke sauke kayayyaki a Legas - NPA

Jiragen ruwa 18 ke sauke kayayyaki a Legas - NPA

- Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa na Najeriya (NPA), ta ce jiragen ruwa 18 ne ke sauke kayayyakin man fetur da kayayyakin abinci a filin jiragen ruwa na Legas

- NPA ta bayyana kayan da ake saukewa wadanda suka hada da alkama, man fetur, takin mai, sukari, man waken soya, nasara da sukari

- Hukumar ta ce wasu jiragen ruwa 15 sun iso filin amma basu fara sauke kayan ba

Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa na Najeriya (NPA), a ranar Litinin ta ce jiragen ruwa 18 ne ke sauke kayayyakin man fetur da kayayyakin abinci a filin jiragen ruwa na Legas.

Hukumar NPA ta sanar da hakan ne a wata wallafar da tayi, kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Tuntuben aiki ya sa mu ka turawa Fasto Omale N573m a akawun – inji Banki

NPA ta bayyana irin kayan da ake saukewa wadanda suka hada da alkama, man fetur, takin mai, sukari, man waken soya, nasara da sukari.

Jiragen ruwa 18 ke sauke kayayyaki a Legas - NPA
Jiragen ruwa 18 ke sauke kayayyaki a Legas - NPA Hoto: Businessday
Asali: UGC

Hukumar ta ce wasu jiragen ruwa 15 sun iso filin amma basu fara sauke kayan ba.

Hukumar ta kara da cewa tana tsammanin isowar wasu jiragen ruwan 12 dankare da kayayyakin man fetur, kayan abinci da sauran abubuwan bukata a ranar 10 ga watan Augusta.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram ta halaka farar hula 223 da jami'an tsaro 89 a cikin wata 7

A wani labarin kuma, shirin gwamnatin tarayya na Solar Homes Systems (SHS), da ke karkashin tsarin ESP, zai kashe N2.3trn wajen samar da hasken lantarki a kauyukan Nigeria.

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan, yana mai cewa, shirin SHS zai samar da cibiyoyin sarrafa hasken rana zuwa wutar lantarki ga gidaje miliyan 5.

A cewarsa, idan aka samar da kananun cibiyoyin, hakan zai sa akalla mutane miliyan 25 su amfana da hasken lantarkin a kauyukan da ke fadin Najeriya.

Osinbajo, a taron tattauna tsare tsaren gwamnatin tarayya na 2020 a cibiyar kasuwanci da masana'antu ta Lagos (LCCI), ya ce gwamnati ta ware N2.3trn domin samar da hasken lantarkin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel