Bidiyo: Wata mata ta daure dan kishiya tsawon shekara biyu a turken tumaki

Bidiyo: Wata mata ta daure dan kishiya tsawon shekara biyu a turken tumaki

Wata mata ta daure yaro maraya mai shekaru 10, mai suna Jibril Aliyu, na tsawo shekaru biyu a garken tumaki ba tare da abinci isasshe ba a jihar Kebbi.

Jaridar Daily Nigerian ta gano cewa, matar uban yaron ta dinga yi mishi tamkar ba dan Adam ba bayan rasuwar mahaifiyarsa.

Wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumuntar zamani a sa'o'in farko na ranar Litinin, wanda ke nuna yaron a rame har baya iya tashi tsaye saboda yunwa.

Jaridar Daily Nigerian ta gano cewa, an damke wacce ake zargin yayin da aka kwantar da yaron a asibitin tunawa da Yahaya da ke Birnin Kebbi.

Bidiyo: Wata mata ta daure dan kishiya tsawon shekara biyu a turken tumaki
Bidiyo: Wata mata ta daure dan kishiya tsawon shekara biyu a turken tumaki. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Facebook

Wani bidiyo wanda ake zargin an daukesa a ofishin 'yan sanda a jihar, ya bayyana wacce ake zargin tana bayani ga 'yan sanda inda take musanta daure yaron.

Kamar yadda wata ma'abocin amfani da Facebook, Tukur Tacha, ya wallafa, ya ce mahaifiyar yaron ta rasu a shekarun da suka gabata kuma ana zargin marikiyarsa da ciyar da shi da ragowar abinci da kuma kashin tumaki.

KU KARANTA: Gwamna ya kori hadiminsa sa'o'i kadan bayan shagalin bikin diyarsa

Wata ma'abociyar amfani da kafar sada zumunta ta Facebook mai suna Maryam Shetty, ta kushe halayyar matar da ta zarga da rashin nuna nadama tare da kwatanta ta da shaidaniya.

Ta ce: "Bidiyon wata shidaniyar mata da ta daure maraya na tsawon shekaru biyu kamar akuya gaskiya ne. Yana fama da yunwa don da ragowar abinci da kashin dabbobi take ciyar da shi. Rashin tausayi..."

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kebbi, ya tabbatar da kamen wacce ake zargin tare da cewa matar tana hannun 'yan sanda.

Kamar yadda yace, idan aka kammala bincike, za a gurfanar da ita a gaban kotu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: