Dole ne mu tattausawa mamatanmu - Tinubu ya yi ta'aziyyar Kashamu

Dole ne mu tattausawa mamatanmu - Tinubu ya yi ta'aziyyar Kashamu

Bola Tinubu, babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC)) na kasa, ya ce mutuwar Buruji Kashamu na nuna cewa mutuwa rigar kowa ce.

Kashamu, tsohon Sanata daga jihar Ogun, ya mutu sakamakon annobar korona a asibiti a jihar Legas a ranar Asabar, 8 ga watan Agusta.

A wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi, Tinubu ya ce ya matukar girgiza kuma ya yi jimamin mutuwar Kashamu wanda ya bayyana a matsayin "fitaccen shugaba a kasar nan kuma dan siyasa na gaske".

Dole ne mu tattausawa mamatanmu - Tinubu ya yi ta'aziyyar Kashamu
Dole ne mu tattausawa mamatanmu - Tinubu ya yi ta'aziyyar Kashamu Hoto: Thisday
Asali: Depositphotos

Ya ce mamacin ya yi aiki tukuru wurin ci gaban siyasa da tattalin arzikin jihar Ogun, ya kara da cewa yana matukar sha'awar kokarin Kashamu duk da ba jam'iyyar su daya ba.

Tinubu ya ce mutuwar Kashamu ya kara yawan manyan mutanen da kasar nan ta rasa sakamakon annobar covid-19.

KU KARANTA KUMA: Mataimakin gwamnan Edo ya yi zargin cewa wasu manya na shirin kashe shi

"Ya yi yaki ga kansa, jama'ar jihar Ogun da kuma kasar nan baki daya," Tinubu yace.

"Sanata Kashamu mutum ne nagari. Ba ya sassautawa wurin goyon bayan jam'iyyar sa ta PDP duk da hawa da gangaren da ya fuskanta a rayuwar siyasarsa. Mutuwarsa babbar rashi ce ga siyasar Najeriya.

"Ya yi matukar kokari wurin ci gaban siyasa da tattalin arziki a jihar. Kashamu ya wakilci yankin Ogun ta gabas a majalisar dattawa karo ta takwas kuma ya yi kokari a mazabarsa."

Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya da suka ci gaba da kiyaye dokokin dakile yaduwar korona ta yadda sauran harkokin tattalin arziki za su ci gaba.

"Ina mika ta'aziyyar ga iyalansa. Allah ya gafarta masa ya kuma karesu a kowanne lokaci," Tinubu yace.

Ya mika ta'aziyyarsa ga Dapo Abiodun, gwamnan jihar Ogun da kuma jama'ar jihar baki daya.

A gefe guda, Legit.ng ta ruwaito cewa, tsohon shugaban kasa Obasanjo a ranar Asabar, 8 ga watan Augusta, ya mika takardar ta'aziiyarsa ga gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, a kan mutuwar Sanata Buruji Kashamu.

A wasikar mai kwanan wata Asabar, 8 ga Augusta, tsohon shugaban kasar ya bayyana mutuwar Kashamu a matsayin rashin da ba za a iya mayar da shi ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel