Ganduje ya kudiri aniyyar tallafawa malaman makarantu masu zaman kansu a Kano

Ganduje ya kudiri aniyyar tallafawa malaman makarantu masu zaman kansu a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da cewa, za ta ba da tallafi ga malamai da ma’aikatan makarantu masu zaman kansu domin rage raɗaɗin mummunan tasirin da annobar korona ta yi a kansu.

Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje, ya zayyana hakan ne yayin kaddamar da fara rarraba kayayyakin kare kai daga kamuwa da cutar korona ga makarantu 538 da suka hadar da na gwamnati da na masu zaman kansu.

Ganduje wanda mataimakinsa, Nasir Yusuf Gawuna ya wakilta, ya ce mamallakan makarantu masu zaman kansu sun yi wa gwamnati korafi a kan kalubalen da ma’aikatansu suke fuskanta a wanda annobar korona ta yi sanadi.

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta wallafa, Gawuna ya ce gwamnatin za ta duba lamarin domin ganin ta kawo mafita.

Dangane da rarraba kayayyakin kariya, Ganduje ya ce hakan yana cikin shirye-shiryen da gwamnatin jihar ke yi a kan komawar dalibai ‘yan ajin karshe makarantun da za su zana jarrabawa.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano
Asali: UGC

A cewarsa, daga cikin kayayyakin kariyar akwai takunkumin rufe fuska, sunadarin tsaftace hannu (sanitizer) botikan wanke hannu karkashin ruwa mai gudana da kuma na’urar daukan dumin jiki.

Ganduje ya kara da cewa, gwamnatin jihar tana kan gabar cin nasara a fagen yaki da cutar korona da ta sanya a gaba.

Ya kira yi mazauna jihar da su yi taka-tsan-tsan wajen kiyaye ka’idodi da matakan da mahukuntan lafiya suka shar’anta domin dakile bazuwar kwayoyin cutar.

Ganduje y ace gwamnati ta tilasta sanya takunkumin rufe fuska ko ina a fadin jihar ba wai kawai sai a makarantu ba. Ya ce nan ba jimawa za a tsananta aiki da dokar a jihar.

Ya kira yi shugabannin makarantu, malamai da sauran ma’aikata, da su tabbatar sun yi tattali tare da amfani da kayayyakin kariyar da gwamnati ta rarraba ta hanyoyin da suka dace domin hana yaduwar cutar a tsakanin dalibai.

Cikin nasa jawaban, kwamishinan ilimi na jihar, Sanusi Kiru, ya ce gwamnatin Kano ita kadai ce cikin dukkanin jihohin da ke fadin tarayya da ta dauki nauyin rarraba kayayyakin kariya a makarantu.

KARANTA KUMA: Buhari ya yaba wa Tambuwal da Sultan kan tsaro a Sakkwato

Alhaji Kiru ya ce kayayyakin kariyar da gwamnatin ta rarraba sun dace da bukatar kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar korona.

Yana mai cewa, daga cikin dalibai 27,454 ‘yan ajin karshe da za su zana jarrabawar kammala karantun sakandire ta WAEC a bana, 11,400 su ne ‘yan makarantun gwamnati yayin da 16,640 suka kasance na makarantu masu zaman kansu.

Kwamishinan lafiya na jihar, Ibrahim Tsanyawa, y ace za a tantace dukkan dalibai kuma sannan za a tabbatar kowanne ya wanke hannu tare da sanya takunkumin rufe fuska gabanin shiga makarantu da dakin jarrabawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel