APC ta lashe zaben maye gurbi na jihar Nasarawa

APC ta lashe zaben maye gurbi na jihar Nasarawa

Dan takarar jam'iyyar APC, Isma'il Danbaba, ya yi nasarar lashe zaben maye gurbi na mazabar Nasarawa ta tsakiya a majalisar jihar.

Baturen zabe na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, Iliyasu Umar, ya sanar da sakamakon zaben maye gurbin da aka yi a ranar Aasbar a garin Nasarawa.

A yayin sanar da sakamakon, Umar ya ce dan takarar jam'iyyar APC ya samu kuri'a 7,475 inda ya buge Bage Nuhu na jam'iyyar PDP mai kuri'u 4,608.

Ya ce a yayin zaben maye gurbin, an kada kuri'a 12,217, amma amintattu sune 12,083 ne kacal yayin da aka soke 134.

"Sakamakon karfin iko da aka bani na baturen zaben nan, ina bayyana dan takarar jma'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri'u mafi rinjaye," yace.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta sanar da sake yin zaben mazabar Nasarawa ta tsakiya ne bayan rasuwan dan majalisa mai wakiltar mazabar, Alhaji Suleiman Adamu, a ranar 30 ga watan Afirilu.

APC ta lashe zaben maye gurbi na jihar Nasarawa
APC ta lashe zaben maye gurbi na jihar Nasarawa. Hoto daga Punch
Asali: UGC

KU KARANTA: Mai Deribe: Mamallakin fadar zinari a Najeriya da ke saukar manyan shugabannin duniya

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya bayyana cewa jam'iyyarsu ta Peoples Democratic Party (PDP), za ta lashe zabe a 2023.

A wata hira da gwamnan ya yi da sashin Hausa na BBC, ya ce kawunan yan jam'iyyar APC duk a rarrabe yake, cewa sun hadu ne ta wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari kawai.

Da aka tambaye shi kan yadda yake ganin zaben PDP a 2023, Gwamna Bala ya ce: “Mu dai mun san jam’iyyar APC hadin gambiza ce, na mutane wanda suke mayaudara, kuma wanda su zo suka hada kawunansu daga wurare daban-daban, kuma wanda suke har yanzu kansu a rarrabe ne.

"Abunda ya hada su kawai mutum daya ne, shine mai gida Muhammadu Buhari shugaban kasa. Kuma zai gama mulkinsa a 2023, saboda haka abunda ya hadasu ya raba. Yanzu ka ga kowa yana magana a kan zama shugaban kasa duk kansu a rarrabe."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel